Luca Modric ya kusan buga wa Real Madrid wasa 500

An wallafa

Luca Modric ya cika shekara 38 da haihuwa ranar Asabar, wanda aka haifa a Zadar a Croatia ranar 9 ga watan Satumbar 1985.

Mai taka leda daga gurbin tsakiya a Real Madrid ya buga wa kungiyar ta Sifaniyar wasa 492 da daukar kofi 23.

Tsohon dan kwallon Tottenham ya koma Santiago Bernabeu a kakar 2012/13 daga kungiyar da ke buga Premier League.

Ranar 27 ga watan Agusta Real ta sanar da ta cimma yarjejeniyar daukar dan kwallon Tottenham kan fam miliyan 30.

Daga nan Modric ya saka hannu kan kwantiragin kaka biyar da kungiyar ta Sifaniya.

Kwana biyu tsakani ya fara buga wa Real tamaula a karawa da Barcelona a zagaye na biyu a Spanish Super Cup a 2012 a Santiago Bernabeu, inda ya maye gurbin Mesut 0zil in the 83rd minute.

Ya ci kofina 23 da Real ciki har da Champions League biyar da Club World Cups biyar da European Super Cups hudu da Leagues uku da Copa del Rey biyu da kuma Spanish Super Cups hudu.

Rawar da yake takawa a tawagar Croatia da ta Real Madrid ta sa ya lashe manyan kyautuka a fannin tamaula a duniya.

Ya lashe kyautar Ballon d'Or da ta fitaccen dan kwallon kafa na duniya na FIFA duk a 2018.

Modric, wanda ke cikin 'yan takarar Ballon d'Or na 2022/23 yana kaka ta 12 a Real Madrid da cin kwallo 37 a wasa 492 da ya yi.