Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Vinicius Junior zai yi jinyar mako shida a Real Madrid
Dan wasan Real Madrid Vinicius Junior zai yi jinyar mako shida sakamakon raunin da ya ji, in ji rahotanni daga jaridun Sifaniya.
Real Madrid ta tabbatar da cewar dan kwallon tawagar Brazil ya ji rauni, amma ba ta fayyace kwanakin jinyar da zai yi ba.
Vinicius ya ji rauni a karawa da Celta Vigo ranar Juma'a, inda Real ta ci 1-0 a gasar La Liga, kuma kungiyar ta lashe dukkan wasa uku da ta a fara kakar bana.
Mai shekara 23 ba zai murmure ba kafin Champions League da za a fara a ranar 19 ga watan Satumba.
Ke nan ba zai yi wa Real wasan La Liga da yawa ba, ciki har da na karawa da Real Sociedad da na hamayya da Atletico Madrid.
Rahoton da jaridun Sifaniya suka wallafa ya ce dan wasan zai yi jinyar tsakanin wata daya zuwa mako shida.
Sannan ba zai buga karawa hudu ba a babbar gasar tamaula ta Sifaniya da kuma wasa daya a Zakarun Turai.