Liverpool ta amince za ta ɗauki Chiesa daga Juventus

Federico Chiesa

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Liverpool ta amince da farashin da Juventus ta yi na sayar mata da Federico Chiesa.

Ƙungiyar Anfield ta amince za ta biya £10m ga ɗan wasan tawagar Italiya da karin £2.5m, idan ya taka rawar gani.

Chiesa, mai shekara 26, zai je Anfield a auna koshin lafiyarsa, idan an kammala komai zai zama na farko da Arne Slot ya ɗauka a Liverpool.

Yana cikin ƴan wasan tawagar Italiya da suka lashe Euro 2020, bayan doke Ingila a Wembley a wasan karshe.

Ya ci ƙwallo 32 a wasa 131 a Juventus har da 10 a lik a karawa 37 a kakar da ta wuce.

Sabon kociyan Juventus, Thiago Motta, bai yi amfani da Chiesa a karawa biyu da fara gasar Serie A ba ta kakar nan.

Liverpool ta kuma ɗauki golan, Georgia, Giorgi Mamardashvili daga Valencia kan £29m - amma zai ci gaba da taka leda a Sifaniya, sai a baɗi ne zai koma Anfield.