Yamal zai yi jinya Lewandowski zai yi hutun kwana 10

Yamal Lewandoeski

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Barcelona ta sanar cewar Lamine Yamal ya ji rauni a kafarsa ta dama, bayan da likitoci suka auna koshin lafiyarsa ranar Litinin.

Ana sa ran zai yi jinya tsakanin mako biyu zuwa uku, kafin ya koma fagen fama.

Shi kuwa Lewandowski na jin raɗadi a gadon bayansa, inda Barcelona ta ce zai yi hutun kwana 10.

Ƴan wasan biyu suna daga cikin fitattu a Barcelona a kwazon da take yi a bana karkashin Hansi Flick tare da Raphinha.

Waɗan nan uku sune kan gaba a yawan zura ƙwallaye a manyan gasar Turai a kakar nan.

Lamine ya ci ƙwallo shida a wasa 15, shi kuwa Lewandowski ya sharara 17 a dukkan karawa a bana, shi ne kan gaba a La Liga a yawan cin ƙwallaye.

Ranar Lahadi Real Sociedad ta doke Barcelona 1-0 a wasan mako na13 a La Liga.

Karon farko da Sociedad ta yi nasara a kan Barcelona, tun bayan ranar Asabar 9 ga watan Afirilun 2016 da ta ci 1--0 shima a gida.

Duk da hakan Barcelona ta ci gaba da zama ta ɗaya a kan teburi, amma da tazarar maki shida tsakani da Real Madrid ta biyu.

Haka kuma shi ne wasa na biyu da aka doke Barcelona a La Liga a bana daga karawa 13, tun bayan wanda Osasuna ta caskara ta 4-2 ranar 28 ga watan Satumba.

Kuma wasa na uku da aka ci Barcelona a dukkan karawa a kakar nan, bayan 2-1 da Monaco ta yi nasara ranar 19 ga watan Satumba a Faransa a Champions League.