Man United ta je ta ci Luton 2-1 a Premier ranar Lahadi

An wallafa

Manchester United ta je ta ci Luton 2-1 a wasan mako na 25 a Premier League ranar Lahadi.

Ana fara wasa Rasmus Hojlund ya ci kwallo, sannan minti shida tsakani ya kara na biyu.

A minti na 14 ne Luton ta zare daya ta hannun Carlton Morris.

Sai dai tun kan hutu United tayi rashin mai tsaron baya, Luke Shaw, wanda ya ji rauni, yayin da aka sauya Harry Maguire da Casemiro lokacin hutu.

Da wannan sakamakon United ta hada maki 44 tana ta shida a teburin Premier League, saura maki biyar tsakaninta da gurbin ƴan hudu da Aston Villa ke kai.

Ita kuwa Luton mai maki 20 tana ta 17 a kasan teburin babbar gasar tamaula ta Ingila da tazarar maki daya tsakaninta da Everton ta ukun karshe.

Ranar Litinin za a kammala karawar mako na 25, inda Crystal Palace za ta je gidan Everton a Goodison Park.

Litinin 19 ga watan Fabrairu 2024

  • Everton da Crystal Palace

Kwantan wasan mako na 18

Talata 20 ga watan Fabrairu 2024

  • Manchester City da Brentford