Juve da Napoli na son Jorginho, Ko Zidane zai tafi Man Utd?

Asalin hoton, Getty Images
Ɗanwasan tsakiya na Arsenal da Italiya Jorginho, mai shekara 32, na jan hankalin Juventus da Lazio da Napoli da ke ribibinsa yayin da kwangilar shi ke dab da ƙarewa. (Standard)
Sabon daraktan wasa na Manchester United mai jiran gado Dan Ashworth ya gana da tsohon kocin Chelsea da Brighton Graham Potter yayin Erik ten Hag ke ci gaba da fuskantar matsi. (Sun)
Zinedine Zidane ba ya da sha'war zuwa Ingila domin yana da wahala ya karɓi aikin horar da Manchester United idan har ƙungiyar ta nemi shi don ya maye gurbin Ten Hag. (The i)
Liverpool ta fara harin kocin Brighton Roberto de Zerbi idan har ta gaza ɗauko kocin Bayer Leverkusen Xabi Alonso domin maye gurbin Jurgen Klopp. (Guardian)
Burnley za ta ci gaba da aiki da Vincent Kompany ko da kuwa an kori ƙungiyar daga gasar Firimiya a bana. (Football Insider)
Barcelona ta tuntubi kocin Portugal Roberto Martinez domin maye gurbin Xavi da zai tafi a ƙarshen kaka. (Football Transfers)
Aston Villa za ta sayar da ƴanwasa da dama domin kauce wa saɓa dokar Firimiya yayin da Newcastle ke son matashin ɗanwasan tsakiya na Ingila mai shekara 22- Jacob Ramsey, Arsenal kuma na son ɗanwasan tsakiya na Brazil Douglas Luiz, mai shekara 25. (Mail)
Chelsea da West Ham da Juventus da AC Milan da Nice da Lyon na ribibin ɗanwasan baya na Ingila da Gent mai shekara 21 Archie Brown. (Standard)
AC Milan na sa ido kan golan Arsenal da England Aaron Ramsdale, 25 domin maye gurbin Mike Maignan na Faransa. (Ekrem Konur)
Liverpool na da yaƙinin ɗanwasan baya na Scotland Andy Robertson, mai shekara 29, zai ci gaba da taka leda a ƙungiyar duk da Bayern Munich ta nuna sha'awarsa. (Football Insider)
Tottenham da Borussia Dortmund na sa ido kan ɗanwasan gaba na Togo da Cercle Brugge Kevin Denkey, mai shekara 23. (Foot Mercato - in French)
Aston Villa na nazarin sayen ɗanwasan baya Faransa Clement Lenglet da ta karɓo aro daga Barcelona. (Mundo Deportivo - in Spanish)











