Madrid na son dawo da Varane da Casemiro, ko Alonso zai tafi Liverpool?

,,

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Real Madrid ta fara nazarin dawo da ɗanwasan baya na Faransa Raphael Varane, mai shekara 30, da kuma ɗanwasan tsakiya na Brazil Casemiro, mai shekara 32, waɗanda ta sayar wa Manchester United.(Fichajes - in Spanish)

Shugaban La Liga Javier Tebas ya ce yiyuwar ɗanwasan Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 25 ta zuwa Real Madrid ta kai kashi 99 idan har ya bar Paris St-Germain a wannan bazara. (L'Equipe - in French)

Manchester City ta ce darajar ɗanwasan tsakiyarta Kevin de Bruyne, mai shekara 32 ta kai fam miliyan 100 bayan ya ja hankalin ƙungiyoyin Saudiyya. (Talksport)

Tottenham ta tattauna da Chelsea kan ɗanwasan tsakiya na Ingila Conor Gallagher a Janairu yayin da Spurs ke son ɗauko ɗanwasan a wannan bazara. (Football Insider)

Liverpool ta fara diba yiyuwar ɗauko kocin Sporting Lisbon Ruben Amorim, mai shekara 39 da Julian Nagelsmann na Jamus idan har ta gaza ɗauko kocin Bayer Leverkusen Xabi Alonso domin maye gurbin Jurgen Klopp. (Telegraph - subscription required)

Daraktan wasanni na Barcelona Deco ya ce ƙungiyar ba za ta sayar da ɗanwasan tsakiya na Netherlands Frenkie de Jong, mai shekara 26 ba, da kuma ɗanwasan baya na Uruguay Ronald Araujo, mai shekara 24. (Goal)

Ɗanwasan baya na AC Milan da Faransa Theo Hernandez, mai shekara 26 na cikin zaɓin da Bayern Munich dibawa domin maye gurbin ɗanwasan Canada Alphonso Davies, mai shekara 23, idan har ya ki sabunta kwangilar shi. (Sky Germany)

Leeds United na son ɗawo da ɗanwasan tsakiya na Ingila Kalvin Phillips idan har ƙungiyar ta hauro gasar Firimiya. Ɗanwasan na taka leda a West Ham a matsayin aro daga Manchester City.(Football Insider)

Arsenal da Manchester United da Tottenham na hamayya kan ɗanwasan tsakiya na Fenerbahce Sebastian Szymanski yayin da AC Milan da Inter Milan suka nuna sha'war ɗanwasan na Poland. (Teamtalk)

Ɗanwasan gaba na Manchester United Mason Greenwood, mai shekara 22, na son ci gaba da taka leda a Getafe, a cewar shugaban kungiyar Angel Torres. Ɗanwasan ya tafi Spain ne a matsayin aro. (Metro)