Yadda taron sauyin yanayi na COP27 zai shafi duniya

.
An wallafa

Nan gaba kaɗan ne cikin watannan shugabannin ƙasashen duniya za su taru domin tattauna matakan kare ɗumamar yanayi a taron Majalisar Ɗinkin Duniya kan sauyin yanayi da za a gudanar a ƙasar Masar.

Shekara guda bayan da duniya ta fuskanci bala'o'in da ke da alaƙa da sauyin yanayi da ƙaruwar zafin da ba a taɓa gani ba a tarihin duniya.

Mene ne taron MDD kan sauyin yanayi?

Majalisar Ɗinkin Duniya na gudanar da taruka kan sauyin yanayi a kowacce shekara, domin bai wa gwamnatocin duniya damar ɗaukar matakan da suka dace domin rage ƙaruwar ɗumamar yanayi.

Ana yi wa tarukan laƙabi da COPs, wadda a turance ke nufin "Conference of the Parties" wato tarukan ƙasashen duniya waɗanda suka suka sanya hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD a shekarar 1992.

Taron na bana wanda aka yi wa laƙabi da COP27, shi ne taro na 27 da Majalisar Ɗinkin Duniya ke shiryawa kan sauyin yanayi. Za kuma a gudanar da shi a birnin Sharm el-Sheikh na ƙasar Masar daga ranar 6 zuwa 18 ga watan Nuwamba.

Me ya sa ake buƙatar tarukan COPs?

Duniya na ƙara ɗumama sakamakon ƙaruwar amfani da hayaƙi da ɗan adam ke yi musamman daga yahaƙin da ake ƙonawa saboda amfani da man fetir da iskar gas da kuma ma'adinin Coal.

Yanayin zafin duniya ya ƙaru da kashi 1.1C kuma ya doshi 1.5C, kamar yadda masana kimiyyar sauyin yanayi na MDD, da kuma Majalisar gwamnatocin duniya kan sauyin yanayi (IPCC) suka bayyana.

Idan zafin duniya ya ƙaru da kashi 1.7 zuwa 1.8. IPCC ta yi hasashen cewa rabin al'umar duniya za su fuskanci barazar ci gaba da rayuwa saboda tsananin zafi da raguwar kaɗawar iska.

Domin kare aukuwar hakan, ƙasashe 194 sun rattaɓa hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris a 2015, tare da alƙawarta haɗa hannu domin hana zafin duniya ƙaruwa da kashi 1.5C

.

Asalin hoton, Reuters

Su wane ne za su halarci taron na COP27?

An gayyaci gwamnatocin ƙasashe fiye da 200. To sai dai wasu shugabannin manyan ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki ciki har da shugaban Rasha Vladimir Putin ba za su halarci taron ba. To amma ana sa ran halartar wakilai daga ƙasar.

Haka kuma wasu ƙasashen ciki har da China kawo yanzu ba su tabbatar da cewa ko shugabanninsu za su halarci taron ba.

Mai masaukin baƙi ƙasar Masar ta yi kira ga ƙasashen duniya da su ajiye bambancin ra'ayi da na siyasa da ke tsakaninsu a gefe guda su kuma nuna ''halin dattako''.

An sa ran kuma ƙungiyoyin kare muhalli, da ƙungiyoyin al'umma, da na 'yan kasuwa da na addinai su ma za su halarci taron.

Me ya sa za ayi taron COP27 a Masar?

Wannan shi ne karo na biyar da ake gudanar da taron sauyin yanayi na COP a nahiyar Afirka.

Yankin da gwamnatocin duniya suka yi amanna cewa zai ja hankalin ƙasashen duniya sakamakon mummunar illar da sauyin yanayi ya yi wa nahiyar. IPCC ta ce nahiyar Afirka ɗaya ce daga cikin ɓangarorin duniya da sauyin yanayi ya yi wa illa.

A halin yanzu, an yi ƙiyasin cewa mutum miliyan 17 ne ke fuskantar ƙarancin abinci a yankin gabashin Afirka saboda matsalar fari.

To amma, zaɓar Masar a matsayin wurin da za a yi taron ya janyo ce-ce-ku-ce. Wasu masu rajin kare 'yancin ɗan adam da masu rajin kare muhalli na cewa gwamnatin Masar ta hana su halartar taron saboda yadda suke sukar ƙasar game da yadda take tafiyar da al'amuran 'yancin dan adam.

Me za a tattauna a taron COP27?

Gabanin taron an buƙaci ƙasashen da su gabatar da tsare-tsarensu kan sauyin yanayi. kawo yanzu kuma ƙasashe 25 ne kaɗai suka gabatar da nasu.

Taron na COP27 zai mayar da hankali kan abubuwa uku: • Rage yahaƙi mai guɓata muhalli • Taimaka wa ƙasashe su magance ɗumamar yanayi • Tallafa wa ƙasashe masu tasowa da kayan aiki, da kuɗi domin ayyukan kare sauyin yanayi.

Shin akwai yiyuwar kasa cimma wasu ɓangarorin?

Kuɗi shi ne babbar matsalar da ke damun taron sauyin yanayi.

A shekarar 2009, manyan ƙasashe masu arziki sun ce za su samar da kuɗi dala biliyan 100 zuwa shekarar 2020, ga ƙasashe masu tasowa domin taimaka musu rage gurɓataccen yahaƙi domin fuskantar dumamar yanayi.

To amma an kasa cimma wannan muradi, inda aka mai da shi zuwa shekarar 2023.

To sai dai ƙasashe masu tasowa na kiraye-kiraye ga manyan ƙasashe masu arzikin masana'antu da su riƙa biyansu 'diyya' samakon illar da hayaƙin da suke fitarwa ke yi wa ƙasashen masu tasowa.

Amma ƙasashen masu arziki sun yi watsi da wannan buƙatar tun a taron sauyin yanayi da aka gudanar a birnin Bonn, bayan da suka fahimci ana ƙoƙarin tilkasta musu biyan daiyya na gomman shekaru.

Tarayyar Turai ta amince a ci gaba da tatauna batun a taron na COP27.

Wacce nasara ake sa ran cimmawa a taron?

Ya danganta ga wanda ka yi magana da shi.

Ƙasashe masu tasowa za su buƙaci a sanya batun biyansu diyya - na gurɓata musu muhalli daga ƙasashe masu arziki - a matsayin ɗaya daga cikin ajendojin taron.

Za su kuma su matsa wajen ganin cewar an saka ranar da za a fara biyansu.

Ƙasashe masu arziki za su buƙaci haɗin kan manyan ƙasashe masu tasowa kamr su China da Brazil, da Indonesiya da Afirka ta kudu, da su rage amfanin da ma'adinin Coal da kuma hayaƙi masu gurɓata muhalli.

Akwai kuma alkawuran da aka yi shekarar da ta gabata a kan batun dazuka, da ma'adinin coal da sauran ma'adinai masu gurɓata muhalli, da ake sa ran ƙasashen duniya za su sanya hannu.

To sai masana kimiyya sun yi amanna cewa shugabannin duniya sun makara, kuma ko me aka cimma a taron COP27 ba zai hana zafin duniya ƙaruwa da kashi 1.5C ba.