Man United za ta je gidan Luton ranar Lahadi a Premier League

An wallafa

Luton za ta karbi bakuncin Manchester United, domin buga wasan makon na 25 a gasar Premier League ranar Lahadi.

Kungiyoyin biyu sun kara a bana a gasar ranar 11 ga watan Nuwambar 2023, inda United ta ci 1-0 a Old Trafford ta hannun Victor Lindelof.

United tana ta shidan teburi da maki 41, ita kuwa Luton Town mai kwantan wasa tana ta 17 a kasan teburi da maki 20.

Luton Town ba ta da sabbin yan ƙwallon da suka ji rauni, watakila sabon ɗan wasan da ta ɗauka, Daiki Hashioka ya buga karawar a karon farko.

Wadanda suka daɗe suna jinya a kungiyar sun hada da Mads Andersen da Marvelous Nakamba da kuma kyaftin, Tom Lockyer.

Har yanzu Manchester United ba ta ce komai ba kan Luke Shaw, wanda ta sauya a wasa a makon jiya lokacin hutu.

Aaron Wan-Bissaka ya ji rauni a wajen atisaye, zai yi jinya tare da Tyrell Malacia da Anthony Martial da Lisandro Martinez da kuma Mason Mount.

KARAWA TSAKANIN KUNGIYOYIN BIYU

Luton Town ta kasa cin United a wasa 12 baya a dukkan karawa, wadda aka doke karo 10 da canajaras biyu.

Wasan karshe da Luton ta karbi bakuncin United a Kenilworth Road sun tashi 1-1 a cikin Afirilun 1992.

LUTON TOWN

Wasa daya Luton ta yi nasara daga karawa biyar baya a Premier League, shi ne wanda ta ci Brighton 4-0 a gida da rashin nasara biyu aka doke ta biyu daga ciki.

Wasa hudu baya da Luton ta buga a gida ta yi rashin nasara ne, wato a Kenilworth Road.

Ta zura kwallo a wasa 11 a jere a lik tun daga 1-0 da aka doke ta a Old Trafford a cikin Nuwambar 2023 - ta taba yin irin wannan bajintar daga Disambar 1957 zuwa Maris din 1958.

Kungiyar da ba ta zura mata kwallo ba a wasa na 12 a Premier a gida a bana itace Tottenham.

MANCHESTER UNITED

Manchester United na fatan yin nasara karo biyar a wasa a jere a dukkan fafatawa a karon farko tun Janairun 2023.

Kungiyar da Erik ten Hag ke jan ragama ta hada maki shida a Premier a karawar waje a bana - Manchester City ce kan gaba mai takwas sai Arsenal mai bakwai kafin wasannin ranar Asabar.

United ta yi nasara 11 a jere a wasannin da ta kara da sabbin kungiyoyin da suka koma buga Premier League.

Ba a doke United ba a cikin Fabrairu a wasa 25 da ta buga a Premier League, wadda ta yi nasara 16 da canjaras tara - shekara shida kenan rabonda ta yi rashin nasara a cikin watan Fabrairu.

Kwallo bakwai da Scott McTominay ya ci wa United ya sa ta hada maki 12 daga ciki, shi ne kan gaba a wannan kwazon.

Watakila Rasmus Hojlund ya zama na shida da zai ci kwallo a jere a Premier League kamar yadda Cristiano Ronaldo da Ruud van Nistelrooy da kuma Eric Cantona.