Croatia ta kai Quarter finals bayan cin Japan a bugun fenariti

Asalin hoton, Getty Images
Croatia ta kai wasan daf da na kusa da na karshe, bayan da ta doke Japan da ci 3-1 a bugun fenariti a Gasar Cin Kofin Duniya da ake yi a Qatar.
Japan ce ta fara cin kwallo daf da za a je hutu ta hannun Daizen Maeda, bayan da suka koma zagaye na biyu ne Croatia ta farke ta hannun Ivan Perisic.
Haka suka tashi minti 120 ba wadda ta kara kwallo a raga a wasan zagaye na biyu ranar Litinin.
A bugun fenariti ne Japan ta barar da guda uku ta hannun Takumi Minamino da Kaoru Mitoma da kuma Takuma Asano.
Croatia ta ci kwallaye ta hannun Nikola Vlasic da Marcelo Brozovic, yayin da Marko Livaja ya barar da ta sa.
Daga baya Mario Pasalic mai taka leda a Atalanta ya ci wa Croatia kwallo na uku da ya kai ta quarter finals da ci 3-1.
Ranar Juma'a Croatia za ta buga wasan daf da na kusa da na karshe da duk wadda ta yi nasara tsakanin Brazil da Korea ta Kudu.











