Man City za ta sayar da Laporte ga Al-Nassr ta Saudi Arabia

Aymeric Laporte

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Manchester City ta amince za ta sayar da dan kwallon tawagar Sifaniya, Aymeric Laporte ga Al-Nassr ta Saudi Arabia.

Mai shekara 29, ya buga karawa 43 a kakar 2021/22, sai dai koci, Pep Guardiola yafi amfani da Manuel Akanji da Nathan Ake da yawa a kakarda City ta lashe kofi uku.

Haka kuma City ta dauki dan kwallon tawagar Croatia, mai shekara 21 a bana kan fam miliyan 77.

Laporte zai jeSaudi Arabia, domin taka leda tare da Cristiano Ronaldo da Sadio Mane da Marcelo Brozovic da kuma Alex Telles a kungiyar Al-Nassr.

City ta dauki Laporte a 2021 daga Athletic Bilbao a Janairun 2018 kan fam miliyan 57 a matakin mafi tsada a kungiyar a lokacin.

Ya buga wasa 51 a 2018/19 da kuma yin karawa 44 a 2021/22, sannan City ta dauki Ake da Akanji.

Laporte ya buga karawa 180 jimilla a City da cin kwallo 12 da yi wa Sifaniya karawa 22 da lashe Uefa Nations League a watan Yuni.

Al-Nassr ta dauki Cristiano Ronaldo cikin watan Disamba, wanda ya zama na hudu daga fitattu da gasar Saudi Arabia ta dauka domin taka leda a can.

Daga nan ne kungiyar ta dauki wasu 'yan kwallon da suka hada da Mane da Brozovic da Telles da kuma Seko Fofana a kakar nan.