Yadda yaki tsakanin Iran da Isra'ila zai iya dagula Gabas ta Tsakiya

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Mahmoud El Naggar
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Arabic
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Yakin da Isra'ila ke yi da kungiyar Falasdinawa ta Hamas ya haifar da zaman dar-dar a yankin Gabas ta Tsakiya.
Masu taka rawa ko taimaka wa bangarorin rikicin ta bayan fage, kamar Iran da masu alaka da ita a yankin su ma sun shigo cikin rikicin.
Iran ta musanta hannunta a harin da Hamas ta kai wa Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba, to amma ta nuna goyon bayanta ga abin da ta kira gagarumar girgizar kasa a Isra'ila.
Da farko dai Iran ba ta yi fito-na-fito ba kai tsaye da Isra'ila. To amma Isra'ila ta samu kanta a rikici kai tsaye da kungiyoyin da Iran ke tallafa wa.
Kungiyoyin sun hada da Hezbollah a Lebanon, da 'yan Houthi da ke Yemen, da dai kungiyoyi da dama masu gwagwarmaya da makamai a Iraqi.
Da dama daga cikin wadannan kungiyoyi Amurka da Birtaniya da sauran kungiyoyi sun ayyana su a matsayin kungiyoyin ta'adda.
Rawar da Hezbollah ke takawa a rikicin

Asalin hoton, Reuters
Yakin Gaza ya sake rura wutar zaman dar-dar da ake yi tsakanin Isra'ila da Hezbollah, kuma daga nan Hezbollah ta fara kai hari kan yankunan arewacin Isra'ila a matsayin goyon baya ga Hamas.
Nan da nan Isra'ila ba tare da wani jinkiri ba sojojin Isra'ila suka fara mayar da martani a kan yankunan da Hezbollah, ta ke lamarin da ya kai ga jikkata wasu 'yan Lebanon, kamar yadda sojojin Lebanon suka bayyana.
Su ma 'yan Houthi sun shiga yakin
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kusan wata daya da far yakin Gaza kungiyar ‘yan Houthi ta Yemen ta shiga rikicin, inda ranar 14 ga watan Nuwamba jagoran Houthin, Abdul-Malik al-Houthi ya ce kungiyar za ta rika kai hari kan jiragen Ruwan Isra’ila ko kuma wadanda kamfanonin Isra’ila suka mallaka.
Daga baya ma kungiyar ta ‘yan Houthi ta fadada harin nata inda ta ce duk wani jirgi da zai je Isra’ila ma ba za ta kyale shi ba.
Wannan matakin ya sa jiragen ruwa suka sauya hanya inda suke bin wata mai nisa sosai, kuma wannan ya yi tasiri sosai a kan harkokin kasuwanci na duniya.
Daga irin wannan hari ne kungiyar ta ce ta kai hari kan wasu jiragen ruwa na Isra’ila da suka bijire wa gargadin sojin ruwa na kungiyar.
Makonni kafin wannan daman kungiyar ta kama wani jirgin ruwa mallakar wani dan kasuwa na Isra’ila.
A wani martani na hadakar kasashen duniya, na kare jiragen ruwa a watan Janairu na wannan shekara Amurka ta kai wani hari na sama a Yemen, bayan harain da ‘yan Houthin suka kai kanw ani jirgin ruwan dakon mai na Birtaniya a mashigar Tekun Yemen.
Isra'ila ta fara kisan manya a Lebanon

Asalin hoton, EPA
Yanayin da ake ciki ya ta’azzara bayan da Isra’ila ta zafafa hare-harenta a Lebanon.
Ranar 2 ga watan Janairun 2024, Isra’ila ta kaddamar da harin sama a yankin kudancin Dahiyeh na babban birnin Lebanon Beirut, inda galibi ‘yan Shi’a ne ke zaune a wurin, inda a harin ta kashe mataimakin shugaban Hamas kuma jagagoranta a Gabar Yamma, Saleh al-Arouri.
Isra’ila ta bayyana Arouri a matsayin gada tsakanin Hamas da Hezbollah.
Kwanakin kadan bayan kisan nashi sai Hezbollah ta kai harin makoman roka kusan 40 a kan sansanin sojin saman a Isra’ila na Meron, inda ta kira hakan da martanin kisan jagoran.
A ranar 8 ga watan Janairu, a wani hari da ta kai ta sama Isra’ila ta hallaka Wissam al-Tawil, wanda shi ne mataimakin kwamandan mayakan Radwan na Hezbollah, bisa zargin cewa shi ne ya kitsa harin da aka kai wa sansanin sojin nata.
'Yan Shi'a na Iraqi ma sun bi sahu
A karshe-karshen watan Janairu an hallaka wasu sojojin Amurka uku tare da jikkata wasu 34 a harin da aka kai musu da jirgi maras matuk a wani sansanin sojin na Amurka a arrewa maso gabashin Jordan, kusa da iyakar Syria.
Jordan ta musanta cewa daga yankinta aka kai harin tana mai cewa daga Syria ne.
Shugaban Amurka Joe Biden ya yi Allah-wadarai da harin yana mai gargadin cewa kungiyoyi masu tsattsauran ra’ayi da Iran ke mara wa baya, wadanda ke zaune a Syria da Iraqi na da hannu a ciki. Kum aya lashi takobin cewa Amurka za ta kama masu hannu a harin.
Kungiyar Kataib Hezbollah, da ke dauke da makamai wadda ke Iraqi, waddda Amurka ta ce rundunar sojin juyin-juya-hali ta Iran ce ke gudanar da ita, ita ta bugi kirji da kai harin. To amma kuma Iran ta musanta daukar nauyin kungiyar.
Shigar Iran rikicin kai-tsaye

Asalin hoton, Reuters
Iran ba ta yarda da wanzuwar Isra'ila ba, to amma a baya ta guji yin fito-na-fito na Isra'ila kai tsaye.
To amma a farkon watan Afirilu Isra'ila ta kai hari kan ofishin jakadancin Iran da ke Damascus, inda ta kashe sojoji da dama na rundunar juyin-juya-hali, cikinsu kuma har da Birgediya Janar Mohammad Reza Zahedi.
Gaba a cikin wannan watan sai Iran ta kaddamar da harinta na farko a kan Isra'ila, inda ta yi amfani da jiragen sama marassa matuka da kuma makamai masu linzami a Negev.
Sai dai sojojin Isra'ila sun ce sun yi nasarar kakkabe makaman kafin su isa cikin yankin Isra'ila.
Ta kuma mayar da martani da kai hare-hare a kan Iran kodayake ba ta fito fili ta ce ita ta kai harin ba.
Hadarin fadada rikicin ga yankin
Daga karshe-karshen want Yuni zuwa farkon watan Yuli na wannan shekara, zaman tankiya tsakanin Hezbollah da Isra’ila ya karu sosai. Kungiyar ta kara zafafa hare-harenta, yayin da kuma take rasa mambobinta inda ake kashe su.
A ranar 7 ga watan Yuli, Hezbollah ta kaddamar da hare-haren roka zuwa arewacin Isra’ila, ciki har da hari a kan sansanin sojin saman a Isra’ila na Meron.
Haka kuma a cikin wannan watan dai an kashe wasu yara 12 da wasu manya a wani harin roka a lokacin da suke was an kwallon kafa a yankin Tuddan Golan da Isra’ila ta mamaye.
Hezbollah ta musanta alhakin kai Karin , amma kuma Isra’ila ta mayr da martini da hare-hare ta sama a kan wurare 7 na Hezbollah a yankin Lebanese.
A watan Yuli, babban fito-na-fito da Isra’ila ta yi da kungiyar Houthi da Iran ke mara wa baya ya kasance ne a lokacin da Isra’ila ta yi Ruwan bama-bamai a kan yankin ‘yan Houthi a tashar jirgin ruwa ta Hodeidah a Yemen.
Harin ya hallaka mutum tara da jikkata wasu sama da 80. Harin ya kasance ne bayan wani harin jirgin sama maras matuki da aka kai Isra’ila, a Tel Aviv inda ya kashe mutum daya da raunata mutum 8.
An kawo karshen wannan watan da kisan gillar da Isra’ila ta yi wa kwamandan Hezbollah, Fuad Shukr, a wani hari ta sama a wajen kudancin Beirut.
Sa’o’i bayan wannan an kashe shugaban Hamas, Ismail Haniyeh, a lokacin da ya kai ziyara Tehran, domin halattar rantsar da sabon shugaban Iran.
Iran ta zargi Isra’ila da kisan, duk da cewa Isra’ila ba ta amsa cewa ita ta kashe shi ba.
Wadannan jerin abubuwa sun kara sa ana ganin wannan zaman tankiya da ya dade ana yi tsakanin Iran da Isra’ila, ka iya kaiwa ga gagarumin yaki na kai tsaye tsakaninsu wanda ka iya fantsama a yankin Gabas ta Tsakiya gabadaya.










