Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lokuta shida da Israila ta mamaye Lebanon
A ranar 18 ga watan Fabairaru wa'adin da aka ɗebar wa Israila game da ficewa daga kudancin Lebanon ya zo ƙarshe , wanda wani ɓangare ne na yarjejeniyar tsagaita wuta da ƙasashen duniya suka gabatar, domin kawo ƙarshen faɗan watanni fiye da 16.
A ƙarƙashin ƙa'idojjin yarjejeniyar, ana sa ran Isra'ila za ta janye dukkanin dakarunta daga yankin Lebanon, kuma an buƙaci ƙungiyar Hezbullah ta 'yan shi'a ta janye dakarunta da makamai daga yankunan da ke kudancin kogin Litani.
Yarjejeniyar ta buƙaci a girke dubban dakarun Lebanon a yanki.
Farmakin na Isra'ila ya yi sanadin mutuwar mutum kusan 4,000 a ƙasar ta Lebanon waɗanda suka haɗa da farar hula tare da tilasta wa mutane fiye da miliyan guda ficewa daga gidanjensu, a cewar hukumomin Lebanon .
Mahukuntan Isra'ila sun ce aƙalla sojoji 80 da farar hula 47 ne aka kashe, yayin da mutane 60,000 suka rasa matsugunansu a cikin ƙasar.
Rikicin baya-baya nan shi ne mafi muni a tsawon shekarun da aka shafe ana zaman doya da manja tsakanin Isra'ila da Hezbullah, kuma wannan ba shi ne karon farko da Isra'ila ta mamaye Lebanon ba.
A lokuta aƙalla biyar Isra'ila ta kai manya-mayan farmaki a kan iyakokin makwabciyar tata da ke arewaci.
1978: Mamaya ta farko (Farmakin Litani)
A ranar 14 ga watan Maris ɗin 1978, Isra'ila ta ƙaddamar da farmaki domin fatattakar mayaƙan ƙungiyar PLO da ke gwagwamayar ƙwato wa Falasɗinawa 'yanci daga kan iyaka, bayan harin sunƙurun da mayaƙan ƙungiyar suka kai wa arewacin Isra'ila daga teku da ya yi sanadin mutuwar farar hula aƙalla 30.
PLO ta maida hedikwatarta Lebanon bayan korar da aka yi mata a ƙasar Jordan a shekarar 1970
Sojojin Israila sun shiga arewaci ƙasar har zuwa kogin Litani, amma ba su samu damar yin arangama da mayaƙan PLO ba, saboda sun ja da baya yayin da sojojin Isra'ilan ke dannawa.
Bayan makonni biyu PLO ta ayyana tsagaita wuta, ita kuma Isra'ila ta janye dakarunta bayan shekara guda, sai dai ta riƙa mara wa wata ƙungiyar mayaƙan sa-kai ta kirista baya da ake kira 'South Lebanon Army' domin tabbatar da tsaro a kan iyakokin wasu yankuna.
A lokacin da farmakin na Litani ya zo ƙarshe a watan Yuni , 'yan Lebanon da Falasɗinawa fiye da 1,000 ne aka ƙiyasta cewa an kashe.
1982: Mamaya ta biyu (Operation Peace for Galilee)
Farmakin farko na Litani bai kawo ƙarshen faɗa tsakanin mayaƙan PLO da sojojin Isra'ila a kan iyaka ba, kuma bayan da wata ƙungiyar Falasɗinawa ta raunata jakadan Isra'ila da harbin bindiga a birnin Landan a ranar 3 ga watan Yuni 1982, sai dakarun Isra'ila ƙarƙashin jagorancin ministan tsaron ƙasar, Ariel Sharon suka ƙaddamar da wani babban farmaki da ya shafi dubban sojojin da ɗaruruwan motoci.
A ranar 6 ga watan Yuni aka soma kai farmaki kuma a cikin kwanaki ƙalilan, sojojin Isra'ila suka shiga wajen garin babban birnin ƙasar inda suka yi wa yammacin Beirut luguden wuta wanda akasarin mazauna wurin musulmi ne.
Mahukuntan Lebanon sun yi ƙiyasin kimanin 'yan Lebanon da Falaɗinawa da farar hula 'yan Syria da kuma mayaƙa 1,900 aka kashe, kodayake akwai waɗanda suka nuna shakku a kan alkaluman.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta rasa sojojinta 376 daga watan Yuni zuwa Satumba 1982.
Sai dai wannan bai kawo ƙarshen zubar da jini ba.
Bayan da aka kashe sabon zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Lebanon wanda kirista ne a wata mota maƙare da bamai-bamai a ranar 14 ga watan Satumba, dakarun Isra'ila sun ba mayaƙan sa- kai na kirista damar shiga sansanonin 'yangudun hijira na Falasɗinawa da ke Sabra da Shattila inda suka kashe farar hula da dama da aka yi ƙiyasin sun kai 700 zuwa 3,500 .
Tare da samun makamai da goyon bayan Iran aka ƙirƙiri ƙungiyar Hezbullah domin yaƙi da sojojin ƙasashen waje.
1993: Farmaki na uku (Yaƙin kwana bakwai na fansa)
An kai wa wuraren Hezbullah hare-haren bama-bamai na tsawon mako guda daga 25 ga watan Yuli.
Isra'ila ta ce ta mayar da martani ne ga hare-haren roka da aka kai wa sansanoninsu da ke Lebanon da kuma arewacin Isra'ila kuma manufar farmakin ita ce a ''taka wa Hezbullah birki don ganin ba ta mayar da kudancin Lebanon sansanin 'yan ta'ada'' ba.
Hezbullah ta yi iƙirarin cewa mayaƙanta sun harba rokoki domin mayar da martani ga hare-haren ta sama da jiragen sama masu saukar ungulu suka kai musu tun farko.
Dubban gidaje ne aka lalata, sai dai Majalisar Dinkin Duniya ta yi ƙiyasin farar hula 130 ne aka kashe yayin da 300,000 suka rasa muhalansu.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce Israilawa biyu tare da sojinta guda aka kashe.
1996: Farmaki na huɗu (Mamaya mai cike da fushi)
Rundunar sojin Isra'ila ta yi amfani da dabara iri guda a farmaki na gaba da ta kai wa Lebanon amma ya ɗauki tsawon lokaci.
Kamar yadda aka saba, rikicin na watan Afrilu ya ɓarke ne bayan da aka harba rokoki cikin Isra'ila, ita kuma ta mayar da martani da ruwan bama-bamai da suka yi sanadin mutuwar mutane 200, galibi farar hula a cewar Makalisar Dinkin Duniya.
Hezbullah ta harba ɗaruruwan rokoki zuwa Isra'ila inda ta raunata farar hula 55 a cewar Majalisar Dinkin Duniya.
2006: Farmaki na biyar
Bayan da mayaƙan Hezbullah suka kama sojojin Isra'ila biyu a ranar 12 ga watan Yuli, sojojin Isra'ila sun kai wa Kudancin Lebanon da Beirut hari ta sama da ƙasa da kuma teku .
A ranar 14 ga watan Agusta ne yarjejeniyar tsagaita wuta da MDD ta shiga tsakani ta fara aiki.
'Yan Lebanon fiye da 1,000 waɗanda galibi farar hula ne aka kashe a yaƙin na tsawon kwanaki 34, tare da sojojin Isra'ila 119 da farar hula 45.
2023: Farmaki na shida (Operation Northern Arrows)
Mayaƙan Hezbullah sun harba rokoki a sansanonin sojin Isra'ila a kan iyakar da ake taƙaddama domin mara wa Falasɗinawa da ke Gaza baya, bayan da aminiyarta Hamas ta kai mumunan hari a Kudancin Isra'ila hari a ranar 7 ga watan Oktoba
A ranar 9 ga watan Oktoba , Hezbullah ta fara kai wa arewacin Israila hari .
Ɓangarorin biyu sun riƙa kai wa juna hari har zuwa ranar 17 ga watan Satumba, lokacin da rikicin ya rincabe a lokacin da na'u'rorin sadarwa na Hizbullah da ake kira Pagers suka riƙa fashewa sakamakon kutsen da Israila ta yi musu.
Haka kuma a ranar 18 ga watan Satumba na'urar sadarwa ta walki-talkies suka tashi, alamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum 39 tare da raunata dubbai a sasan ƙasar
Bayan mako guda da faruwar haka Isra'ila ta ƙaddamar da farmakin da ta yi wa laƙabi da 'Operation Northern Arrows', inda ta riƙa kai hare-hare ta sama kuma a watan Oktoba ta ƙaddamar da farmaki ta ƙasa tana mai cewa tana son ta tabbatar da komawar mazauna 60,000 zuwa arewacin ƙasar cikin aminci waɗanda suka tsere sakamakon hare-haren rokoki.
Jakadan Israila a Majalisar Dinkin Duniya ya ce a ranar 22 ga watan Satumba Hezbullah ta harba rokoki fiye da 8,000 zuwa arewacin Israila da tundan Golan da Isra'ila ta mamaye tun bayan hare haren ranar 8 ga watan Oktoba.
An kashe Hassan Nasrallah, wanda ya jagorancin Hezbollah na tsawon shekara 32 a wani hari ta sama a ranar 27 ga watan Satumban 2024.
Duk da yarjejeniyar tsagaita wuta, Israila ta ci gaba da kai wa sansanonin Hezbullah hari a ƙasar Lebanon tana mai cewa za ta ci gaba da kai wa ƙungiyar hare-hare domin hana ta sake samun makamai.