Rashford ya koma Aston Villa

Asalin hoton, Getty Images
Aston Villa sun kammala ɗaukar ɗa wasan gaba na Manchester United, Marcus Rashford a matsayin aro.
Rashford mai shekara 27 a duniya zai yi wasa a Villa ne har zuwa ƙarshen kakar wasa da ake ciki, kuma ƙungiyar na da damar sayen sa kan kudi fam miliyan 40 idan tana so.
Ɗan wasan ya rubuta a shafinsa na instagram cewa: "Ina gode wa Manchester United da Aston Villa kan cimma wannan yarjejeniya.
"Na yi sa'a ƙungiyoyi da dama sun tuntuɓe ni amma Aston Villa ne wuri mafi sauƙi da zan tafi a yanzu - ina matuƙar sha'awar yadda Aston Villa ke taka leda a kakar bana, da kuma azamar mai horas da ƙungiyar. Abin da kawai nake so shi ne na buga ƙwallo kuma ina farin ciki hakan..
"Ina yi wa duk waɗanda ke a Manchester United fatan alheri a cikin wannan kakar wasanni."







