Liverpool na harin Rodryo, muradin Arsenal kan Goykeres na tangal-tangal

Asalin hoton, Getty Images
Napoli ta sake karkata akalarta kan ɗan wasan Manchester United da Argentina Alejandro Garnacho, mai shekara 21, kuma ta na fatan za ta iya samun ɗan wasan kan farashin fam miliyan 45. (Mirror)
Manchester United na tunanin sayar da ɗan wasan Ingila Jadon Sancho, mai shekara 25, kan farashi mai rahusa. (Givemesport)
United na ci gaba da sa ran cewa za ta iya kammala cinikin ɗan wasan Brentford da Kamaru Bryan Mbeumo, mai shekara 25, ta na kuma fatan ɗan wasan zai kasance a cikin tawagarta kafin ta fara rangadin wasannin share fage a Amurka. (Sky Sports)
Tattaunawar da Arsenal ke yi kan ɗan wasan gaba na Sporting da Sweden Viktor Gyokeres, mai shekara 27, ya tsaya cak sakamakon rashin cimma matsaya kan farashi da kuma sharuɗɗan yarjejeniyar cinikin ɗan wasan. (Independent).
Newcastle United ta yi watsi da tayi na uku da Leeds United ta miƙa kan ɗan wasan tsakiyar Ingila Sean Longstaff mai shekara 27. (Northern Echo).
Al-Hilal na son ɗan wasan gaban RB Leipzig da Slovenia Benjamin Sesko, mai shekara 22, wanda Arsenal ke bibiya. Kungiyar Saudi Pro League ta na kuma zawarcin ɗan wasan gaban Crystal Palace Jean-Philippe Mateta, mai shekara 28. (Sun).
Aston Villa da Brighton sun sanya ido kan ɗan wasan ƙasar Benin Rodolfo Aloko, mai shekara 18, daga NK Kustosija ta Croatia. (Mail).
Nottingham Forest da Crystal Palace suna cikin jerin ƙungiyoyin Premier da ke nazari kan ɗan wasan tsakiya na Manchester City da Ingila na ƴan ƙasa da shekara 21 James McAtee, mai shekara 22. (Sky Sports)
Liverpool za ta iya bin sahun Arsenal wajen fafutukar ɗaukar ɗan wasan gaban Real Madrid da Brazil Rodrygo, mai shekara 24, idan har ta rasa ɗan wasan Colombia Luis Diaz, mai shekara 28, wanda ake alaƙantawa da komawa Barcelona. (Sacha Tavoleri).
Ɗan wasan tawagar Portugal Chiquinho, mai shekara 25, ya bar Wolves ya koma Alverca ta ƙasar Portugal kan kwantiragin din din din, inda kulob ɗin na Premier zai samu kashi 40 cikin 100 na kuɗin da za a sayar da ɗan wasan nan gaba. (Fabrizio Romano)
Brighton ta shirya bai wa Roma aron ɗan wasan Jamhuriyar Ireland Evan Ferguson ga amma har yanzu ƙungiyar ba ta samu amincewa daga ɓangaren dan wasan mai shekara 20 ba. (Calciomercato)











