Abincin gargajiya da gasar tseren ninƙaya cikin hotunan Afirka

c

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A ranar Laraba, ma'aikatan lafiya da ke asibitin Mama Lucy Kibaki a birnin Nairobi na ƙasar Kenya, sun fito kan mattakalan asibitin a lokacin da shugaban adawar ƙasar Raila Odinga ya ziyarci asibitin don duba magoya bayansa da aka ji wa rauni a lokacin zanga-zangar adawa da gwamnatin ƙasar.
An wallafa
c

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Mista Odinga na kira ga magoya bayansa su gudanar da zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa da Ƙaruwar kudin haraji a ƙasar.
x

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wata matashiya kenan ke ninƙaya a gaɓar tekun Masar a ranar Talata
cf

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Masu yawon buɗe idanu ke shaƙatawa a tekun Masar cikin makon da ya gabata.
d

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Shi kuma wannan mutumin ɗan ƙasar Somaliya na ninƙaya ba tare da hawa kwale-kwale ko jirgin ruwa ba a tekun Geelaq da ke gundumar Hamarweyne a birnin Mogadishu ranar Juma'a
d

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A ranar Laraba Lia Ana Lima 'yar Ƙasar Angola ta fafata a gasar ninƙayar mita 200 ta mata da aka gudanar
cv

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A Senegal kuma, wani mai ninƙaya ne ya tsamo waya daga ƙarƙashin teku bayan da wani jirgin ruwa ɗauke da 'yan ci-rani ya kife ranar Litinin
f

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Souhila Belkati 'yar Algeriya ɗauke da 'yarta a cikin gidanta da ya ƙone sakamakon gobarar daji a Bejaia, ranar Talata
x

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Ranar Juma'a a lokacin da wata mata 'yan ƙasar Ivory Coast ke shiƙan garin rogo domin dafa abincin gargajiya a birnin Abidjan.
ds

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wani mai sayar da tsofaffin injinan janareto a birnin Lagos da ke Najeriya.
c

Asalin hoton, CHRIS HYDE/FIFA

Bayanan hoto, 'Yar wasan tawagar ƙwallon ƙafar Najeriya ta mata Asisat Oshoala ke murnar ƙwallon da ta zira a wasan da Najeriya ta doke Austrialiya a gasar ƙwallon ƙafar mata ta duniya da ke gudana a Austrialiya da New Zealand