Man Utd za ta yi gwanjon ƴanwasa 11, Arsenal na son Onana

..

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Ɗanwasan tsakiya na Brazil Casemiro, mai shekara 31 da ɗanwasan baya na Faransa Raphael Varane, mai shekara 30 da ɗanwasan baya na Ingila Harry Maguire, mai shekara 30 na cikin ƴanwasa 11 da Manchester United za ta yi gwanjon su a bazara. (ESPN)

Shugaban Manchester United Sir Jim Ratcliffe, wanda samun gurbin gasar zakarun turai ya ba muhimmanci, yana son ya jira har zuwa ƙarshen kaka kafin yanke hukunci kan makomar kocin ƙungiyar Erik ten Hag. (Star)

Manchester United na iya ba Thomas Tuchel aikin horar da ƴanwasanta wanda zai bar Bayern Munich a ƙarshen kaka. (Sky Germany)

Liverpool ta faɗawa Chelsea cewa ɗanwasanta na gaba na Uruguay Darwin Nunez, mai shekara 24 ba na sayarwa ba ne. (Times - subscription required)

Arsenal na son ɗauko ɗanwasan tsakiya na Belgium da Everton Amadou Onana, mai shekara 22 a bazara. (Teamtalk)

Kocin Sporting Lisbon Ruben Amorim zai iya zama kocin Liverpool idan har ƙungiyar ta gaza ɗauko kocin Bayer Leverkusen Xabi Alonso a matsayin wanda zai gaji Jurgen Klopp. (Independent)

Ɗanwasan baya na Tottenham da Ingila Eric Dier, mai shekara 30 da wahala ya ci gaba da taka leda a Bayern Munich har zuwa bazara saboda rashin taka rawar gani. (Bild via Mail)

Manchester City na dab da sabunta kwangilar ɗanwasan gaba na Norway Oscar Bobb, mai shekara 20. (Mail)

Tottenham na nazarin raba gari da ɗanwasan tsakiyarta Pierre-Emile Hojbjerg, mai shekara 28, yayin da ƙungiyoyin Italiya suka nuna sha'awar ɗanwasan na Denmark. (Football Insider)

Arsenal na son ɗauko matashin ɗanwasan Rangers Alexander Smith. (Sun)

Brighton da Celtic na cikin ƙungiyoyi da dama da ke sa ido kan matashin ɗanwasan gaba na Charlton Athletic mai shekara 18 Patrick Casey. (Football Insider)

Ɗanwasan tsakiya na Turkiyya Hakan Calhanoglu, mai shekara 30, ya ce an tuntuɓe shi a Saudiyya amma ya fi son ya ci gaba da taka leda a Inter Milan. (DAZN, via Gazzetta dello Sport)