Real Betis ta ɗauki aron Antony daga Man United

Antony

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ɗan wasan Manchester United, Antony zai koma buga wasannin aro a gasar La Liga a ƙungiyar Real Betis zuwa karshen kakar bana.

Mai shekara 24 ɗan kasar Brazil ya koma United daga Ajax a Agustan 2022 kan £81.3m - na biyu mafi tsada a tarihinta bayan Paul Pogba.

Ya ci ƙwallo 12 a wasa 96 da ya yi wa United, amma yanzu ɗaya ya zura a raga a Premier League tun daga Afirilun 2023.

Wata majiya daga United ta ce a yarjejeniyar za a biya albashin Antony da zai kai £100,000 a duk mako

Yana da kwantiragi da United har zuwa karshen kakar 2027..

Antony ya fara taka rawar gani karkashin koci, Erik ten Hag da cin ƙwallo uku a wasa uku da ya fara a Premier League.

Daga baya ɗan wasan ya koma baya kokari da ta kai ya koma zaman benci, wanda ya yi karawa 13 a bana a United a wasa 33 da ta yi a dukkan fafatawa.