An sauya ranar da Arsenal ya kamata ta je gidan Newcastle

Arsenal

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Mahukutan Premier League sun canja ranar da Arsenal ya kamata ta ziyarci Newacastle United a wasa na biyu a babbar gasar tamaula ta Ingila.

Tun farko an tsara cewar Gunners za ta ziyarci St James Park ranar Asabar 6 ga watan Mayu, yanzu ya koma ranar Lahadi 7 ga watan Mayu.

Mahukuntan sun ce sun yi hakan ne domin haska wasan a talabijin, domin yana daya daga cikin wadanda sa suyi zafi a gasar Premier League a makon.

Kungiyoyin biyu sun kara a wasan farko a Premier ta bana a Emirates, inda suka tashi 0-0 ranar 3 ga watan Janairun 2023.

Arsenal wadda ta yi wasa 28 kawo yanzu, tana ta daya a kan teburi da maki 69 da tazarar takwas tsakaninta da Manchester City ta biyu, mai rike da kofin bara.

Newcastle tana ta biyar a teburin Premier Leage da maki 47, bayan da ta buga wasa 26.

Arsenal za ta karbi bakuncin Leeds United ranar Asabar 1 ga watan Afirilu a Emirates, sannan ta ziyarci Liverpool ranar 9 ga watan Afirilu.

Ita kuwa Newcastle United za ta karbi bakuncin Manchester United ranar Lahadi 2 ga watan Afirilu, sannan ta je gidan West Ham kwana uku tsakani.

Arsenal na kokarin lashe Premier League na bana a karon farko, tun bayan 2004, karkashin Arsene Wenger.

Sai dai kofin da take fatan dauka kenan a kakar nan, bayan da aka fitar da ita a Europa League da FA Cup, Manchester United ce ta lashe Carabao Cup.

Kofin farko da ta dauka kenan tun bayan 2016/17 karkashin Jose Mourinho, wanda ya dauki League Cup da Europa League.