An yi wa Kroos jan kati a wasan da Real Madrid ta yi 1-1 da Girona

Toni Kroos

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Real Madrid ta raba maki da Girona, bayan da suka tashi 1-1 a wasan mako na 12 a gasar La Liga da suka fafata a Santiago Bernabeu ranar Lahadi.

Saura minti 20 a tashi daga wasan Real ta ci kwallo ta hannu Vinicius Junior.

To sai dai Girona ta farke ta hannun Cristhian Stuani a bugun fenariti, saura minti 10 lokaci ya cika.

Real ta karasa fafatawar da 'yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Toni Kroos jan kati daf da za a tashi daga wasan.

Karo na biyu da Real ta tashi 1-1 a gasar La Liga ta bana, bayan wanda ta yi a gida da Osasuna ranar 2 ga watan Oktoba a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.

Da wannan sakamakon Real Madrid ta koma ta daya a kan teburin La Liga da maki 32 da tazarar maki daya tsakaninta da Barcelona ta biyu.

Ranar Laraba 2 ga watan Nuwamba, Real Madrid za ta karbi bakuncin Celtic a wasan karshe a cikin rukuni a Champions League.

Kafin wannan karawar kungiyoyin sun yi wasa shida a tsakaninsu, inda Real Madrid ta yi nasara a hudu, Girona ta ci wasa biyu.

Karawar da kungiyoyin suka yi:

2018/2019

Spanish La Liga Lahadi 17 ga watan Fabrairun 2019        

  • Real Madrid    1 - 2     Girona

Copa del Rey Alhamis 31 ga watan Janairun 2019

  • Girona 1 - 3     Real Madrid   

Copa del Rey Alhamis 24 ga watan Janairun 2019

  • Real Madrid    4 - 2     Girona

Spanish La Liga Lahadi 26 ga watan Agustan 2018           

  • Girona 1 - 4     Real Madrid   

2017/2018

Spanish La Liga Lahadi 18 ga watan Maris 2018          

  • Real Madrid    6 - 3     Girona

Spanish La Liga Lahadi 29 ga watan Oktoban 2017

  • Girona 2 - 1     Real Madrid   

'Yan wasan da Carlo Ancelotti ya fuskanci Girona a gida.

'Yan wasan Real Madrid:

Masu tsaron raga: Courtois, Lunin, Luis López.

Masu tsaron baya: Carvajal, E. Militão, Alaba, Vallejo, Nacho, Odriozola, Lucas V., Rüdiger, F. Mendy.

Masu buga tsakiya: Kroos, Modrić, Camavinga, Valverde, Tchouameni, D. Ceballos.

Masu cin kwallaye: Hazard, Asensio, Vini Jr., Rodrygo, Mariano.