Man United na fatan sayen mai cin kwallaye in ji Ten Hag

An wallafa

Erik ten Hag ya sanar da cewa Manchester United na fatan sayen ɗan wasa mai cin kwallaye kafin a fara kakar 2023/24.

Kociyan ya ce suna ta neman wanda zai dace da United don kara karfin kungiyar, bayan da ta ɗauki Mason Mount da Andre Onana.

Ana ta alakanta United da wasu fitattun 'yan kwallon da take son dauka, domin fuskantar kakar da za a fara a cikin watan Agusta.

An tambayi Ten Hag kan batun sayen Harry Kane saboda an ji United ba ta ce komai ba kan cinikin, sai ya ce ba zai yi magana kan ɗan kwallon da yake da yarjejeniya da wata kungiya ba.

An kuma tambayi Erik ko United za ta ci karo da kalubalen kuɗi idan za ta sayo wani ɗan wasan, kociyan bai ce komai ba.

Sai dai Ten Hag ya ce alhakin dukkan 'yan wasan United ne kowa ya ci kwallo ba sai mai buga lamba tara ba.

Kociyan ya kara da cewa United za ta kara sa kwazo a kakar bana, duk da cewar ba ta da 'yan wasa da suka ci mata kwallaye da yawa a kakar da ta wuce.

Ten Hag, wanda zai ja ragamar United a karo na biyu ya lashe Caraboa Cup a kakar da ta wuce da yin na uku a Premier League.

United, wadda za ta buga Champions League a kakar bana, za kuma ta fafata a Premier League da FA Cup da kuma League Cup.

Jerin waɗanda suka ci wa United kwallaye a kakar 2022/23

  • Marcus Rashford: Kwallo 30
  • Bruno Fernandes: Kwallo 14
  • Anthony Martial: Kwallo 9
  • Antony: Kwallo 8
  • Casemiro: Kwallo 7
  • Fred: Kwallo 6
  • Jadon Sancho: Kwallo 6
  • Alejandro Garnacho: Kwallo 5