Paris St Germain ta dauki Hugo Ekitike daga Reims

An wallafa

Paris St-Germain ta dauki aron dan kwallon Reims, mai cin kwallaye, Hugo Ekitike kan yarjejeniyar za ta iya sayenshi, idan ya taka rawar gani.

Kamar yadda L'Equipe ta wallafa, PSG ta aminci za ta sayi dan wasan, mai shekara 20 kan fam miliyan 30.6, sai dai wata takaddama tsakanin Ekitike da Reims ta kawo tsaikon kammala cinikin da ya koma zai buga wasannin aro.

Ekitike ya ci kwallo 11 a kakar da ya fara buga wa Reims tamaula a karon farko.

Newcastle United ta yi zawarcin dan wasan tawagar Faransa ta 'yan kasa da shekara 20, amma ta kasa cimma yarjejeniya.

Ekitike, shi ne na uku da PSG ta dauka a bana, bayan Vitinha daga Porto da Nuno Mendes daga Sporting Lisbon, dukkansu kan fam miliyan 34.

PSG ce ta lashe Ligue 1 a kakar da ta wuce, sai dai kuma kungiyar ta sallami kociyanta, Mauricio Pochettino ta kuma maye gurbinsa da Christoper Galtier.

Kungiyar ta Faransa ta kori kociyan dan kasar Argentina, bayan da ya kasa kai PSG matakin sama da zagayen kungiyoyi 16 a gasar Champions League.

Wasan farko da Galtier zai ja ragama a bana shi ne Trophee des Champions da wadda ta ci French Cup, Nantes ranar 31 ga watan Yuli.

Za kuma ta fara wasan farko a kakar babbar gasar tamaula ta Faransa da Clermont ranar 6 ga watan Agusta.