Man City za ta koma kan ganiya - Walker

Kyle Walker

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ƙyaftin ɗin Manchester City, Kyle Walker ya ce yana da tabbacin cewar za su koma kan ganiya, bayan cin karo da koma baya a wasanninsu.

City mai fuskantar kalubale ta yi rashin nasara karo na biyar a jere ranar Asabar, bayan da Tottenham ta doke ta 4-0 a Premier League a Etihad.

Wannan shi ne rashin ƙwazo mafi muni a City tun bayan 2006, kuma karo na uku a jere a Premier League da aka doke ƙungiyar da Pep Guardiola ke jan ragama.

Walker na fatan za su kara sa ƙaimi idan sun zo karawa da Feyenoord a Champions League ranar Talata a Etihad.

Bayan nan City za ta buga wasa mai zafi da Liverpool a Anfield a gasar Premier League, wadda ke fatan lashe kofi na biyar a jere.

''Hakika mun shiga wani yanayin da ba mu saba ganinsa ba, amma za mu saka kaimi domin komawa kan ganiya,'' in ji Walker.

City tana mataki na biyu a kan teburin Premier da maki 23, bayan buga wasan mako na 12, Liverpool ce kan gaba da maki 29.

Jerin wasa biyar da aka doke Man City:

League Cup Laraba 30 ga watan Oktoba

  • Tottenham 2 - 1 Man City

Premier League Asabar 2 ga watan Nuwamba

  • Bournemouth 2 - 1 Man City

Champions League Talata 5 ga watan Nuwamba

  • Sporting 4 - 1 Man City

Premier League Asabar 9 ga watan Nuwamba

  • Brighton 2 - 1 Man City

Premier League Asabar 23 ga watan Nuwamba

  • Man City 0 - 4 Tottenham