Abu biyar kan iƙirarin Putin a 2024

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Ilya Barabanov, Sergei Goryashko, Tom Santorelli
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
Yayin da 2024 ke ƙarewa, Shugaban Rasha Vladimir Putin ya gudanar da taron manema labarai na ƙarshen shekara kamar yadda ya saba, amma akwai wasu muhimman abubuwa da suka zama tarnaƙi ga shugaban.
Mun yi waiwaye kan wasu muhimman abubuwa biyar da suka shafi Vladimir Putin a shekarar 2024.
A jawabin da ya gabatar a ranar 19 ga Disamba, shugaban na Rasha ya taɓo batutuwa da dama kamar tattalin arziki da raguwar yawan haihuwa da Donald Trump da kuma yaƙi Isra'ila a Gaza.
Amma batun yaƙin Rasha a Ukraine ne ya mamaye jawabin shugaban na tsawon sa'a huɗu da rabi, kuma yayin da ake shiga shekara ta uku a yaƙin, ya yi ƙoƙarin nuna nasarorin da ya samu a tsawon watanni 12.
Ya sanar da cewa sojojin Rasha "sun kama.. da ƙwato yankunan da aka ƙwace," kuma suna samun nasara a fagen daga a "kullum", yana mai bayyana dakarunsa a matsayin jarumai tare da cewa ya kare ƙasar Rasha.
Kodayake ya sha yin watsi da tsagaita wuta, amma ya nuna cewa zai iya aminta da wasu matakai domin kawo ƙarshen yaƙin - amma ba a san me yake nufi ba. Ya ce Kremlin a shirye take ta tattauna da Kiev ba tare da wasu sharuɗɗa ba, amma ya nanata iƙirarinsa game da haramcin Zelensky.
Amma waɗanne muhimman abubuwa ne biyar da Vladimir Putin bai yi magana a kai ba - kuma wane tasiri suka yi?
Mutuwar Alexei Navalny
A ranar 16 ga watan Fabrairun 2024, madugun adawar Rasha Alexei Navalny, ya mutu a arewacin Rasha, kuma har yanzu mutanensa na ci gaba da binciken musabbabin mutuwarsa, yayin da wasu da dama ke tunanin shugaba Putin ne ya bayar da umarnin kisan shi bayan an taɓa yunƙurin kashe shi ta hanyar guba.

Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock
A lokacin Moscow da wasu ƙasashen Turai na tattaunawa kan musayar fursunoni, wanda aka gudanar da ranar 1 ga Agusta.
Bayan Rasha ta ƙaddamar da mamayar Ukraine, a lokacin ta soma kama ƴan ƙasarta kan duk wani kalami da ya shafi nuna adawa da yaƙin.
Navalny, wanda ke yawan sukar yaƙin, ya ci gaba da yi duk da yana kulle a gidan yari.
Mutuwarsa ta yi tasiri sosai ga dubban mutanen Rasha.
Harin gidan casu na Crocus City
Duk da hankalin hukumomin Rasha ya karkata kan Ukraine da ɗaukar mutane aikin soja da samar da sabbin makamai, amma sun yi biris da ƙaruwar masu tsatsauran ra'ayin addinin Islama, musamman a jihohin da ke tsakiyar yankin Asiya da yankin arewacin Caucasus.
A watan Oktoban 2023, harin ranar 22 ga watan Maris 2024 da aka kai a filin jirgin sama na Makhachkala na ɗaya daga cikin mafi muni a tasirin Rasha wanda aka kai a yankin Moscow.
Mutum 145 aka kashe yayin da 551 suka jikkata a harin gidan casu na Crocus City Hall, ɗaya daga cikin hari mafi muni tun bayan harin makarantar Beslan, da ya faru shekara 20 a lardin Moscow.

Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock
Mayaƙan Vilayat Khorasan na Afghanistan sun yi iƙirarin ɗaukar nauyin harin, amma farfagandar Rasha da Vladimir Putin sun ɗora harin kan Ukraine.
Sun yi iƙirarin cewa maharan na son tserewa zuwa Ukraine bayan harin inda aka yi masu tanadin hanyar ficewa a kan iyaka.
Babu wata shaida da aka gabatar, kuma babu wasu hukumomin Ukraine da aka tabbatar kan zargin.
Maharan ga alama suna ƙoƙarin tserewa ne zuwa Belarus domin hawa jirgi - amma hukumomin Rasha sun ci gaba da zargin Ukraine kuma shugaban bai fadi harin ba a cikin jawabinsa.
Syria

Asalin hoton, Reuters
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Bashar al-Assad ya samu taimakon sojojin Rasha a tsawon shekara tara. Tun 2015 sojojin Rasha suka tafi can, kuma Assad ya ci gaba da zama kan mulki da kuma nasarar IS - da aka haramta a Rasha.
Sai dai yayin da hankalin Rasha ya karkata kan yaƙin Ukraine, Moscow ba ta da lokacin Syaria ko Bashar al-Assad.
Sakamakon haka mayakan HTS suka samu sa'ar hamɓarar da gwamnatin Assad a Damascus cikin kwana 10 wanda ya tilasta wa Assad neman mafaka a Rasha inda zai yi rayuwa da irin Viktor Yanukovych, tsohon shugaban Ukraine da shi ma ya tsere.
Faɗuwar gwamnatin Assad labari ne marar daɗi ga Kremlin musamman rasa sansanonin sojin Rasha a Syria a biranen Latakia da Tartus, wanda hakan illa ne ga tasirin Rasha a Gabas Ta Tsakiya.
Putin ya daɗe yana iƙirarin cewa zai mayar da Rasha babbar mai faɗa a ji a duniya amma yaƙin da ya fara ya sa ƙasashen musamman makwabtanta ba su buƙata.
Duk da haka, ya yi amfani da jawabinsa ga ƴan ƙasa domin ƙarfafa ra'ayinsa cewa Rasha ba ta yi rashin nasara ba a Syria. A cewar Putin, Rasha ta cimma muradunta a Syria tare da hana kafa Daular Musulunci, amma ya amincewa cewa lamarin akwai "sarƙaƙiya"
Ya ce har yanzu bai yi magana ba da hamɓararren shugaban Syria wanda ya tsere zuwa Moscow.
Ya ƙara da cewa Rasha na tattaunawa da sabbin shugabannin Syria domin ikon muhimman sansanonin sojin Rasha.
Makamin Oreshnik
Dab da ƙarshen 2024, lokacin da dakarun Ukraine da aminansu ke ratsawa ta yankin Rasha kusan a kullum, Kremlin ta yi masu barazana da makamin nukiliya wato makamai mai linzame na Oreshnik.
Zuwa yanzu, lokacin da kawai aka taɓa amfani da Oreshnik shi ne tsakiyar Nuwamba a garin Dnepr na Ukraine. An yi iƙirarin cewa an yi amfani da shi ne a matsayin martani ga harin makami mai linzame mai cin dogon zango na ƙasashen Turai da aka kai yankin Rasha. Tun lokacin Putin da masu farfagandar Rasha sun jinjina wa makamin.
A jawabinsa, Putin ya yi barazanar cewa Rasha na iya harba Oreshnik zuwa cikin Ukraine, idan har makaman Ukraine na iya kakkaɓo shi.
Babu ranar da Putin ba ya ambatar makamin a jawabinsa tun lokacin da aka soma amfani da shi.
Amintaka da Kim Jong-un
A ƙarshen 2023, Kremlin ta ƙulla kawancen soji da Koriya ta Arewa, ƙasar da Rasha da sauran mambobin kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya suka ƙaƙaba wa takunkumi. Da farko saboda ƙarancin makaman atilare da masu linzame a yaƙinta da Ukraine, Moscow ta fara neman taimakon Pyongyang. Maimakon hakan kuma Rasha ta dinga shigar da mai zuwa Koriya ta Arewa.
A 2024, Putin ya gana da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un Pyongyang. Ziyarar da ya kai wa ɗaya daga cikin masu mulkin kama-karya a duniya ita ce a 2000, zamanin mulkin Kim Jong-il, mahaifin Kim Jong-un. A Rasha kuma mutum guda ne ke mulki a tsawon shekarun.

Asalin hoton, SPUTNIK/KREMLIN POOL/EPA-EFE/REX/Shutterstock
Bayan ganawa da shugabannin biyu suka yi, ƙasashen biyu sun amince da yarjejeniyar yauƙaƙa dangantaka tsakaninsu, daga ciki har da samar da taimakon soji idan har ɗaya daga cikinsu ta samu kanta cikin yaƙi.
Nato ta kiyasta cewa dakarun sun kai mutum 12,000, haka ma hukumomin Ukraine sun faɗi nasu binciken.
Amma Moscow da Pyongyang sun musanta kasancewar dakarun Koriya Ta Arewa a yaƙin Ukraine. A ƙarshen watan Oktoba, Putin ya yi tsokaci cewa Rasha yanzu na samun taimakon makamai da kuma soji daga Koriya Ta Arewa, yana mai yin nuni da yarjejeniyar da suka ƙulla, da ya kira kasuwancinsu.
Kasuwancin na sojojin Koriya Ta Arewa ya shafi ƙoƙarin ƙwato yankunan Kursk da Ukraine ta ƙwace a Agusta. Zuwa disamba, rahotanni sun ce an kashe ɗaruruwan ƴan Koriya ta Arewa ko jikkata su. Wannan yaƙi ne da ba su da masaniya sai daga baya. Kafofin yaɗa labarai na ƙasar ba su ce komi ba a shekarar farko.
Nato na kallon shigar Koriya ta Arewa a yaƙin Ukaine a matsayin wani mataki na takalar faɗa.
Wata babbar majiyar BBC a Nato ta nuna tasirin hakan zai shafi fagen daga.
Ma'aikatar harakokin wajen Amurka ta yi imanin babbar aminiyar Rasha - China - ba ta ji daɗin ƙawancen Moscow da Pyongyang ba.











