Barcelona ta lashe Spanish Super Cup bayan caskara Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona ta lashe Spanish Super Cup na bana, bayan da ta caskara Real Madrid da cin 5-2 ranar Lahadi a filin wasa na King Abdullah a Saudi Arabia.
Cikin waɗanda suka ci wa Barcelona ƙwallayen sun hada da Lamine Yamal da Robert Lewandoeski da Alejandro Balde da kuma Raphinha da ya zura biyu a raga.
Real Madrid ta zare biyu ta hannun Kylian Mbappeda da Rodrygo a wasan farko na El Clasico da suka yi a 2025.
To sai dai Barcelona ta kare karawar da ƴan wasa 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa mai tsaron raga, Wojciech Szczęsny jan kati, saboda keta da ya yi wa Mbappe.
Wannan shi ne karon farko da kociyan Barcelona, Hansi Flick ya ɗauki kofi a ƙungiyar, wanda ya karɓi aiki kan fara kakar bana daga Xavi Hernandez.
Wannan shi ne karon farko da Barcelona ta zura ƙwallo biyar a ragar Real Madrid tun bayan 5-1 da ta ci a La Liga ranar 28 ga watan Oktoban 2018.
A kakar bana, Barcelona ta je ta doke Real Madrid 4-0 a cikin watan Oktoba a gasar La Liga a Santiago Bernabeu.
A bara ne Real Madrid ta lashe Spanish Super Cup, bayan da ta doke Barcelona 4-1 a Saudi Arabia ranar 14 ga watan Janairun 2024.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Bayan kammala Spanish Super Cup, Real Madrid za ta buga Copa del Rey zagayen ƴan 16 da Celta Vigo a Santiago Bernabeu ranar Alhamis 16 ga watan Janairu.
Daga nan kuma Las Palmas za ta kai wa Real Madrid ziyara a La Liga ranar Lahadi 19 ga watan Janairu.
Itama Barcelona za ta kara a Copa del Rey da Real Betis ranar Laraba 15 ga watan Janairu, sai ta je Getafe ranar Asabar 18 ga watan Janairu a La Liga.
Barcelona ce kan gaba a yawan ɗaukar Spanish Super Cup mai 14 da tazarar ɗaya tsakaninta da Real Madrid.
Wasa 11 baya na El Clasico da aka fafata tsakanin Real da Barca:
12/10/24 (SUPER CUP )
- Real Madrid 1-5 Barcelona
26/10/24 (LIGA)
- Real Madrid 0-4 Barça
21/04/24 (LIGA)
- Real Madrid 3-2 Barça
14/01/24 (SUPER CUP)
- Real Madrid 4-1 Barça
28/10/23 (LIGA)
- Barça 1-2 Real Madrid
05/04/23 (COPA DEL REY)
- Barça 0-4 Real Madrid
19/03/23 (LIGA)
- Barça 2-1 Real Madrid
02/03/23 (COPA DEL REY)
- Real Madrid 0-1 Barça
15/01/23 (SUPER CUP)
- Real Madrid 1-3 Barça
16/10/22 (LIGA)
- Real Madrid 3-1 Barça
20/03/22 (LIGA)
- Real Madrid 0-4 Barça
Ƴan wasan Real Madrid da suka fuskanci Barcelona:
Masu tsare raga: Courtois, Lunin and Fran González.
Masu tsare baya: Alaba, Lucas Vázquez, Fran García, Rüdiger, Mendy, Asencio, Lorenzo and Diego Aguado.
Masu buga tsakiya: Bellingham, Camavinga, Valverde, Modrić, Tchouameni, Arda Güler and Ceballos.
Masu cin ƙwallaye: Vini Jr, Mbappé, Rodrygo, Endrick, Brahim and Yáñez.











