Kai Havertz zai shafe watanni yana jinya

Ɗanwasan gaba na Arsenal Kai Havertz

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ɗanwasan gaba na Arsenal Kai Havertz ya tafi jinya har sai an kammala kakar bana bayan samun rauni a ƙafarsa lokacin wasannin atisaye a Dubai.

Tafiyar ɗanwasan babban giɓi ne ga Arsenal ba tare da tsayayyen ɗanwasan gaba ba har zuwa ƙarshen kakar bana.

Wasu majiyoyi sun ce ɗanwasan zai buƙaci tiyata bayan ya dawo tare da tawagar ƙungiyar a ranar Talata.

Arsenal ba ta ce komi ba game da raunin da Havertz ya ji ba. Ana sa ran kocin ƙungiyar Mikel Arteta ya yi bayani game da girman raunin idan zai gana da manema labarai a ranar Juma'a kafin wasan Arsenal da Leicester City ranar Asabar.

Gabriel Jesus ma ya yi fama da rauni a guiwarsa inda aka yi masa tiyata, haka ma Bukayo Saka an yi masa tiyata a watan Disamba.

Havertz ya haska sau 34 a wasannin Arsenal a bana kuma shi ya fi cin kwallo a kakar bana inda ya zura 15 a raga kuma ya taimaka aka ci biyar.

Ana ganin dai raunin babban ƙalubale ne ga Arsenal musamman wajen cin ƙwallaye bayan ƙungiyar ta gaza ɗauko ɗanwasan gaba a Janairu.

Arsenal ce ta biyu a teburin Premier, tazarar maki bakwai tsakaninta da Liverpool.