Mourinho ya maka Galatasaray a kotu

Asalin hoton, Getty Images
Jose Mourinho ya ɗauki matakin shari'a a kan Galatasaray, bayan da ta zarge shi da kalaman wariyar launin fata.
An zargi kociyan, Fenerbahce ne sakamakon kalaman da ya yi, bayan tashi wasan hamayya na ƴan birnin Istanbul ranar Litinin.
Ranar Talata Galatasaray ta fitar da jawabin cewar kalaman ɗan kasar Portugal bai dace ba, wanda baya kan ka'ida.
Ranar Juma'a, Fenerbahce ta sanar cewar Mourinho ya shigar da karar a biya shi Lira 1,907, 000 kuɗin Turkiya, saboda zarginsa da Galatasaray ta yi da cewar an taɓa mutuncinsa.
Ƙudin da Mourinho ya bukata a biya shi ya kai £41,000 kwatankwacin shekarar 1907 da aka kafa ƙungiyar Fenerbahce.
Bayan da aka tashi daga wasan na hammaya 0-0 ranar Litinin, Mourinho ya ce masu masauƙin baki sai murna suke suna ''tsalle kamar birrai.''
Haka kuma ya caccaki alkalan tamaula na Turkiya da cewar da wani daga ciki ne ya busa karawar da sai an tashi da takaddama.
Alkalin kasar Slovenia, Slavko Vincic ne ya busa karawar, sakamakon da ƙungiyoyin suka amince a gayyato wani daga wajen kasar.
Ranar Alhamis, hukumar kwallon kafar Turkiya ta dakatar da Mourinho jan ragamar wasa huɗu da biyarn tarar £35,194, bisa wasu mataki biyu na ladabtarwa.











