Biden: Mohammed bin Salman na da alhakin kisan Khashoggi

President Biden was pictured fist-bumping the Saudi crown prince before their talks

Asalin hoton, Reuters

An wallafa

Shugaban Amurka Joe Biden ya tattauna da Mohammed bin Salman, Yarima mai jiran gado na masarautar Saudiyya - matakin da ka iya gyara dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.

Mista Biden ya ce sun tattauna kan wasu muhimman batutuwa, ciki har da ci gaba da tsagaita wutar da ake yi a yakin Yemen da kisan dan jaridar nan Jamal Khashoggi a ofishin jakadancin Saudiyya da ke birnin Santanbul na kasar Turkiyya a 2018.

Wannan tafiyar ta shugaban Amurkar dai ta rika cin karo da matsaloli, kuma da wuya Amurka ta sami dukkan abubuwan da ta so daga Saudiyya duk da cewa shugabanta da kansa ya tafi da kokon bara.

Hukumomin leken asiri na Amurka sun yi imani cewa Yarima Mohammed bin Salman ne ya bayar da umarnin a kashe Jamal Khashoggi.

Matar da Mista Khashoggi ya so ya aura ta wallafa hoton ganawar shugabannin biyu a Twitter, tana tambayar ko wannan ne adalcin da Mista Biden yayi alkawarin karbo wa dan jaridar da aka yi wa mummunar kisan gilla?

Shugaba Biden ya ce ya bayyana wa Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman yadda yake kallon kisan da aka yi wa Mista Khashoggi.

"Kan batun kisan Khashoggi, na tabo mayar da shi cikin manyan batutuwan da muka tattauna a kai, kuma na bayyana masa abin da ke cikin zuciyata a wancan lokacin, da yadda nake kallon abin a yanzu."

Shugaba Biden ya kuma ce, "na gaya masa kai tsaye cewa babu yadda wani shugaban Amurka da zai iya yin shiru kan irin wannan batu na take hakkin dan Adam, domin yayi hannun riga da ainihin yadda muke da kuma yadda na ke. zan ci gaba da kare wannan matsayar tamu a koda yaushe."

To wace amsa Yarima Mohammed ya mayar wa Mista Biden?

"Ya ce min ba shi da hannu kan al'amarin, ni kuma na ce masa a ganina yana da alhaki. Ya ce ya dauki mataki kan wadanda suka aikata laifin."

Amurka dai na kokarin sake kulla dankon zumuntar da ke tsakaninta da kasashen yankin Gabas ta Tsakiya bayan da rikicin Rasha da Ukraine da wanda ke tsakanin Amurka da China suka karkatar da alkiblar Amurka a siyasar duniya.