Roberto de Zerbi zai bar Brighton bayan wasan Man United

Roberto de Zerbi

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Roberto de Zerbi zai bar Brighton bayan buga wasan karshe a Premier League da za su karbi bakuncin Manchester United ranar Lahadi.

Shugaban ƙungiyar, Tony Bloom ya sanar cewar sun cimma yarjejeniya da kociyan dan ƙasar Italiya da su raba gari a tsakaninsu.

De Zerbi, tsohon kociyan Shakhtar Donetsk mai shekara 44, ya karbi aikin jan ragamar Brighton cikin Satumbar 2022 kan yarjejeniyar shekara hudu.

Brighton ta kammala kakar bara a mataki na shida gurbi mafi girma da kungiyar ta taka, hakan ya ba ta damar shiga gasar zakarun Turai karon farko a tarihinta.

A gasar zakarun Turai din ta bana, Brighton ta yi nasara a kan Ajax da Marseille da AEK Athens, wadda ta yi ta ɗaya a teburin rukuni.

Daga baya ne aka yi waje da kungiyar dake buga Premier League a zagayen ƴan 16, bayan rashin nasara a hannun Roma.

A kakar bana ƙungiyar tana ta 10 a teburin Premier League, wadda koda ta buga wasan karshe ranar Lahadi ba damar ta haura matakin da take a yanzu haka.