Ba tabbas kan makomar Ederson a Man City - Guardiola

Ederson

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Kociyan Manchester City, Pep Guardiola ya ce baya da tabbas ko Ederson zai ci gaba da taka leda a ƙungiyar Etihad a bana.

Ana ta alakanta mai tsaron ragar tawagar Brazil da cewar zai koma tamaula a babbar gasar tamaula ta Saudi Arabia.

Guardiola ya sanar a karshen kakar da ta wuce da cewar Ederson ne zai ci gaba da tsare ragar City, amma kuma sai ya yi amfani da Stefan Ortega a wasan farko zagayen kwata fainal da Real Madrid a Champions League.

A lokacin da ya gana da ƴan jarida bayan da Celtic ta doke City 4-3 a wasan sada zumunta a Amurka, Guardiola ya ce ''Zan so ya ci gaba da zama a Etihad, amma hakan ya alakanta daga wasu ƙungiyoyin.''

Ederson ya shiga wasan da Celtic ta doke City a Chapel Hill a zagaye na biyu, shi ne wasan farko da mai rike ta Premier ta yi na shirin tunkarar kakar bana.

Bayan da ake tantama kan makomar Ederson, shi kuwa Kalvin Phillips zai je wata ƙungiyar domin buga wasannin aro kafin a rufe kasuwar cinikin ƴan ƙwallo ranar 30 ga watan Agusta.

Philips ya buga wasannin aro a West Ham United a zagaye na biyu a kakar da ta wuce.