Netanyahu ya gana da Joe Biden na Amurka a fadar White House

..

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Firaiministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya gana da shugaban Amurka, Joe Biden a fadar White House, kwana ɗaya bayan gabatar da wani jawabi mai zafin gaske ga majalisar dokokin ƙasar.

Netanyahun yana kuma shirin saduwa da mataimakiyar shugaban na Amurka, Kamala Harris wadda ake sa ran ta zama ƴar takarar jam'iyyar Democrat a zaɓen shugaban ƙasar na Nuwamba.

Ana dai sa ran cewa mista Netanyahu zai tattauna dangane da batun tsagaita wuta a Gaza da kuma musayar fursunoni.

Rahotanni dai na cewa akwai yiwuwar Mista Biden ka iya tursasa Netanyahu ya sa hannu a kan yarjejeniyar ta tsagaita wuta a lokacin ganawar tasu.

Mista Netanyahu dai na fuskantar matsin lamba a gida da waje na ganin ya kawo ƙarshen yaƙin da Isra'ila a Gaza, a daidai lokacin da yake yawon neman goyon bayan ƴan siyasar Amurkar.

"Maƙiyanmu makiyanku ne," in ji shi.

ya kuma ya amfani da damar da ya samu inda ya soki masu zangza-zangar nuna adawa da yaƙin na Isra'ila a Gaza, waɗanda ya kira "wawayen da Iran ke amfani da su".

..

Dubban maso goyon Falasɗinawa ne dai suka hau titunan birnin Washinton domin ƙalubalantar Mista Netanyahu a matsayin "wanda jinin al'umma ke wuyansa sakamakon yaƙi."

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

An kama mutum 23 ranar Laraba da suka haɗa da biyar waɗanda aka kama a farfajiyar majalisar dokokin Amurkar kamar dai yadda ƴan sanda suka ce.

Mista Netanyahu ya samu jinjina da tafi a lokacin jawabin nasa daga mafi akasari ƴan jam'iyyar Republican.

Yaƙin Gaza dai ya janyo ɓaraka da rabuwar kai a Amurka kuma abin ya janyo rikicin cikin gida tsakanin ƴan jam'iyyar Democrat inda ɓangaren masu son kawo sauyi ke sukar goyon bayan da Amurkar ke bai wa Isra'ila.

An gano ƴar majalisar dokoki Rashida Tlaib cikin ƴan kallo tana ɗaga allo mai ɗauke da rubutun "mai alhakin kisan kiyashi".

Misis Harris ba ta halarci jawabin na Netanyahu ba sakamakon cin karo da ya yi da wasu ayyukan da take gudanarwa a Fadar White House.

Kamala ta kashe rabin ranar tana wata ganawar da wata ƙungiyar baƙar fata.

To sai dai misis Harris ta bayyana cikakken goyon baya ga Isra'ila. Amma ana yi wa matsayin kallon wanda zai iya janyo wa jam'iyyar Democrat bakin jini.

Dubban ɗaruruwan masu zanga-zanga da ke son a dakatar da aikewa da sojojin Amurka zuwa ga Isra'ila sun bayyana rashin goyon bayansu a lokacin zaɓen cikin gida

Wasu ƴan jam'iyyar ta Democrat da matsayin Mista Biden kan yaƙi ke baƙantawa rai na yi wa Misis Harris kallon wadda za ta gyara irin ƙyamar da ake yi wa jam'iyyar.

Ana dai sa ran Mista Netanyahu zai ziyarci ɗan takarar shugabancin Amurka na jam'iyyar Republican, Donald Trump a gidansa da ke Mar-aLago a jihar Florida ranar Juma'a.