Netanyahu na tsaka-mai-wuya bayan Biden ya haƙura da takarar shugaban ƙasa

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Barbara Plett Usher
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Jerusalem
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu na yin ziyara a Amurka a wannan makon yayin da yake tsaka da shan matsi wajen kawo ƙarshen yaƙin da suke yi a Zirin Gaza.
Ko ta yaya guguwar siyasar da ke kaɗawa a Amurka za ta shafi ziyarar tasa da kuma alaƙar Isra'ila da ƙasar?
Mista Netanyahu zai gana da Biden - idan ya warke daga cutar korona - sannan ya yi wa zaman haɗin gwiwa na majalisun ƙasar jawabi, wanda shi ne zai zama shugaban wata ƙasa da ya taɓa yin hakan a karo huɗu.
Balaguron zai ba shi damar sake ƙulla alaƙa da Amurka bayan shafe watanni yana nuna tsaurin ra'ayi a yaƙin na Gaza, inda zai yi ƙoƙarin shawo kan Isra'ilawa cewa ba shi ne ke lalata alaƙa tsakaninsu da babbar ƙawar tasu ba.
Sai dai matakin da Mista Biden ya ɗauka na janyewa daga takarar shugabancin ƙasa ya shafe labarin balaguron na Mista Netanyahu, wanda hakan ya sa shugaban na Isra'ila ke cikin zullumi game da wanda zai gaji Biden ɗin.
Kafin ya baro gida, ɗaruruwan Isra'ilawa sun yi ta zanga-zangar neman ya zauna a gida domin mayar da hankali kan tattaunawar zaman lafiya da Hamas don sako mutanen da ƙuingiyar ke garkuwa da su.
"Idan har bai saka hannu kan yarjejeniyar da ke kan teburi ba a yanzu, ban ga yadda za a yi ya kama hanyar zuwa yin jawabi ana tsaka da hayaniyar siyasa ba a Amurka," a cewar Lee Siegel, ɗaya daga cikin mutanen da aka sace 'yan'uwansu da suka fita zanga-zangar.
A cewarsa, tafiyar ta siyasa ce kawai, har sai Netanyahu ya daina zama "matsala" ya kuma sanya hannu kan yarjejeniyar tsgaita wutar.
Mista Siegel ya jaddada abin da mutane da yawa suka amince da shi cewa Netanyahu na jan ƙafa ne da gangan domin ya tseratar da kan sa a siyasance bayan ya bijiro da wasu sababbin buƙatu cikin tattaunawar da ake yi daidai lokacin da aka kusa cimma matsaya.

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
An sha zargin firaministan da biye wa ministocinsa biyu masu tsattsauran ra'ayi bayan sun yi barazanar ruguza gwamnatinsa idan ya sake ya amince da buƙatun Hamas.
Irin wannan fahimtar ce ta ƙara fusata fadar White House ta Amurka, wadda ta sanar da sabon tayin yarjejeniyar na yanzu tare da bayyana ƙwarin gwiwar cimma matsaya nan kusa.
Biden na ɗaya daga cikin shugabannin Amurka da suka fi mara wa Isra'ila baya a tarihi, wanda ke bayyana kansa a matsayin mai rajin kafa ƙasar Yahudawa (zionist). Isra'ilawa sun yaba masa kan hakan da kuma ziyarar jajen da ya kai musu 'yan kwanaki bayan harin Hamas.
Sai dai kuma tun daga lokacin, ya fara sarewa da aniyar Netanyahu ta neman "cikakkiyar nasara" a kan Hamas.
Gwamnatin ta Biden na jin haushin Netanyahu saboda yadda yake yin watsi da cikakken tsarin yadda za a kawo ƙarshen yaƙin da zai kai ga kafa ƙasar Falasɗinawa.
Tana jin haushinsa kuma dai game da ƙin yin bakin ƙoƙarinsa wajen kare rayukan fararen hular Falasɗinawa, da ƙara yawan kayan agajin da ake kaiwa Gazan. Gwamnatin na fuskantar ɓacin ran Amurkawa kan yawan Falasɗinawan da ake kashewa a yaƙin, sannan ta damu da yadda yaƙin ke yaɗuwa a yankin.

Yayin da gwamnatin Biden ta mayar da hankali kan ƙoshin lafiyarsa a takarar shugaban ƙasa, masu sharhi na cewa akwai wuya shugaban ya iya cigaba da matsa wa Netanyahu wajen kawo ƙarshen yaƙin.
Amma matakin na Biden ya ƙara ƙarfafa masa gwiwa ne ma, in ji Ehud Barak, tsohon firaministan Isra'ila kuma mai adawa da Netanyahu.
"Ba ɗankoyo ba ne a fannin manufar ƙasashen waje, yana da ra'ayin kansa [saboda] ba ruwansa da irin tasirin hakan zai yi a kan masu jefa ƙuri'a [a zaɓen Amurka]," a cewar Mista Barak yayin hira da BBC.
"Game da Isra'ila, yana jin cewa an sakar masa mara domin ya yi duk abin da yake ganin ya kamata a yi."

Mista Barak ya ce kuskure ne a sake gayyatar Netanyahu don ya yi jawabi saboda Isra'ilawa na zargin sa da gazawar da ta sa Hamas ta kai harin, kuma mutum uku cikin huɗu na 'yanƙasar na neman ya sauka daga muƙaminsa.
"Mutumin nan ba wakilin Isra'ila ba ne na ƙwarai," in ji shi. "Isra'ilawa sun daina amincewa da shi. Kuma da alama hakan ba alama ce mai kyau ba ga Isra'ilawan da ma Netanyahun kansa."
Ko ma wace irin siyasa yake yi da batun, Netanyahu ya haƙiƙance cewa ƙarfin soja za a ci gaba da amfani da shi saboda hakan ya fi karya lagon Hamas.
Jim kaɗan kafin ya bar Isra'ila, ya nuna cewa abin da zai tattauna da Shugaba Biden ke nan.
"Za kuma mu samu damar tattaunawa da shi kan wasu abubuwa masu muhimmanci masu zuwa da suka shafi ƙasashen namu," a cewarsa, "sako duka mutanenmu, karya Hamas, daƙile Iran da ƙawayenta, da kuma tabbatar da cewa duka Isra'ilawa sun koma gidajensu a kudu da arewaci."
Ana sa ran zai cigaba da yaɗa wannan matsayar a jawabinsa na majalisar.
Abin da ke ƙasa shi ne tsare-tsaren Netanyahu sun lalata goyon bayan da yake samu daga duka jam'iyyun Amurka. 'Yan Republican na goyon bayansa, amma kuma wasu 'yan Democrat na sukar sa.
Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Dattawa Chuck Schumer ya haddasa cecekuce a kwanan nan lokacin da ya ce Netanyahu na ɗaya daga cikin masu kawo tsaiko wajen samar da zaman lafiya tsakanin Yahudawa da Falasɗinawa.
"Ina fatan Netanyahu na sane da tunanin 'yanmajalisar da yawa kuma zai yi magana a kansu," in ji Thomas Nides tsohon jakadan Amurka a Isra'ila.
Kamala za ta cigaba da maimaita aniyarsu idan ta zama 'yartakarar shugaban ƙasa a Democrat. Ba za a samu wani sauyi ba a manufofin Amurka; kamar cigaba da bai wa Isra'ila kariya yayin da ake ƙoƙarin kawo ƙarshen rikicin na Gaza da kuma abin da zai faru bayan yaƙin.
Amma ƙila a samu sauyi wajen maganganu kan yaƙin.
Kamala ba ta da wata doguwar alaƙa da Isra'ila irin wadda Biden ke da ita. Ƙarnin da aka haife ta daban ne kuma "akwai yiwuwar za ta fi alaƙanta kanta da ra'yoyin matasan jam'iyyar Democrat," kamar yadda Mick Mulroy, wani tsohon ƙaramin mataimakin sakataren tsaro a Gabas ta Tsakiya.
"Ma'ana ɗaya daga cikin abubuwan da za su faru shi ne dakatar da ba Isra'ila makamai don amfani da su a Gaza," in ji shi.

Asalin hoton, EPA
Netanyahu zai iya yin amfani da ziyarar wajen ɗauke hankula daga yaƙin Gaza zuwa kan Iran, wanda maudu'i ne da yake jin daɗin tattauna shi musamman bayan rikicin baya-bayan nan.

Asalin hoton, Reuters
Za kuma ta ba shi damar ƙulla alaƙa ta kusa da tsohon shugaban ƙasa Donald Trump yayin da ake tsaka da guguwar siyasa.
"Kusan akwai ijima'i cewa Netanyahu ya ƙagu Trump ya yi nasara, yana tunanin cewa zai samu damar aikata duk abin da yake so," kamar yadda Michael Koplow ya bayyana.
Abin jira a gani shi ne ko Biden zai sassauta matsin lambar bayan ya fice daga takara, ko kuma zai yi amfani da sauran kwanakinsa wajen kawo ƙarshen yaƙin Gaza.










