Gwamnan Kano nake son zama ba shugaban jam'iyyar APC ba - Abbas

Abdullahi Abbas ya yi shugabancin jam'iyyar APC har karo uku kuma idan aka sake zaɓen sa zai zama karo na huɗu da yake jagorancin jam'iyyar.

Asalin hoton, Alfindiki/Facebook

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano Abdullahi Abbas ya ce shi burinsa ya zama gwamnan Kano ba sake zama shugaban jam'iyyar APC ba a jihar ta Kano.

Abdullahi Abbas ya shaida wa BBC hakan ne yayin mayar da martani ga ministan ma'aikatar gidaje na Najeriya, Yusuf Abdullahi Ata kan kalamansa na baya-baya nan inda ya yi barazanar ficewa daga jam'iyyar.

Ministan ya yi barazanar ficewa daga jam'iyyar APC muddun aka sake zaɓen shugaban jam'iyyar na Kano, Abdullahi Abbas a matsayin shugaban jam'iyyar na jihar a karo na hudu.

A yanzu haka zafafan kalaman ministan a wani bidiyo sun karaɗe shafukan sada zumunta, wanda wani abu ne da ke ci gaba da tayar da ƙura a siyasar jihar Kano.

Sai dai shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano Abdullahi Abbas ya shaida wa BBC cewa Yusuf Ata 'ba dan jam'iyyar ba ne' sannan sun yi mamakin dalilan da suka sa aka dauko shi har aka ba shi mukamin minista

''Mu a wajenmu 'yan jam'iyya, dama ban dan jam'iyya bane, a Kano gaba daya a karamar hukumarsa ne mu ka yi na uku ''

''Kuma ba mu sani ba aka bashi minista kuma har shugaban kasa mu gaya wa cewa ba dan jam'iyyarmu bane, anti party ya yi muna '' in ji shi.

Hon Abbas ya ce sun yi mamakin mukamin minista da shugaba kasa ya ba shi

'' Muna mamakin yadda aka yi wannan abun wallahi, dan siyasa ne na karamar hukuma kawai''


 Wasu jiga -jigan jam'iyyar APC a kano ciki harda jagoronta Abdullahi Abbas

Asalin hoton, FACEBOOK

Bayanan hoto, Wasu jiga-jigan jam'iyyar APC a jihar Kano

Me Yusuf Ata ya faɗi?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wani bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta, ya nuna ministan ma'aikatar gidaje, Yusuf Abdullahi Ata yana jawabi a tsaye ga magoya baya inda ya yi barazanar ficewa daga jam'iyyar APC a Kano shi da magoyansa matuƙar ba a sauya shugabancin jam'iyyar a jihar ba.

Ministan ya ce furucin jagoran jam'iyyar ne ya jawo faɗuwar jam'iyyar a zaɓen da ya gabata na 2023, kamar yadda ya bayyana a taron masu ruwa da tsaki na ƙaramar hukumarsa ta Fage a jihar Kano.

Ata ya ce, "muna faɗa wa kowa, idan aka mayar da irinsu, duk irinmu fita za mu yi."

Ya ƙara da cewa, "mu an mana tarbiya, mun san waye malami, mun san waye babba. Saboda haka ba za mu sauka daga turbarmu ba. Idan suka dawo da shi, mu za mu fita, kuma na rantse da Allah sai jam'iyyar ta sake faɗi zaɓe," in ji shi.

"Dole a canja, dole a nemo mutanen kirki masu mutunci a ba su saboda ya zama tare da mu, ya yi sha'awar ya sake ba mu."

Da alama dai wannan sabon rikici da ya kunno kai a jam'iyyar ta APC a jihar Kano na kara fito da irin rarabuwar kai da takun tsaka a tsakanin 'yayan jam'iyyar da kan iya shafar tasirin jam'iyyar a jihar ta Kano.