Likitoci sun yi wa golan Barca Ter Stegen aiki cikin nasara

Ter Stergen

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Barcelona ta sanar da cewar likitoci sun yi wa ƙyaftin, Marc-Andre ter Stegen aiki cikin nasara ranar Litinin, sakamakon raunin da ya ji ranar Lahadi a gidan Villareal.

Barcelona ce ta je ta casa Villareal 5-1 a wasan mako na shida a La Liga, kenan ta yi nasara shida a jere da fara kakar bana.

To sai dai Barcelona ba ta fayyace kwanakin da zai yi jinya ba da kuma ranar da zai sake komawa tsare ragar ƙungiyar.

An sauya ɗan kasar Jamus a wasan, sakamakon gwurɗa kafa lokacin da ya kama ƙwallo ya faɗo a kanta, sai ɗaukarsa aka yi a kan gadon marasa lafiya.

Barcelona ta ce za ta fitar da karin bayanai da zarar an yi masa aiki, domin fayyace kwanakin da ɗan wasan mai shekara 32 zai yi jinya.

Ter Stegen ya tsare raga sama da karo 400 a Barcelona tun bayan da ya koma can da taka leda daga Borussia Monchengladbach a 2014.

Ƙungiyar da Hansi Flick ke jan ragama tana matakin farko a teburin La Liga da tazarar maki huɗu tsakani da Real Madrid ta biyu mai maki 14.

Ranar Laraba 25 ga watan Satumba, Barcelona za ta karɓi bakuncin Getafe a wasan mako na bakwai a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.