An tuhumi Man United da rashin da'a bayan yi wa rafli kuri

Asalin hoton, Getty Images
An tuhumi Manchester United da nuna halin rashin da'a lokacin da suka yi wa alkalin wasa kuri a FA Cup karawar da ta ci Fulham.
'Yan wasan United sun kalubalanci alkalin wasa Chris Kavanagh a minti na 71 a lamarin da ta kai aka kori Aleksandar Mitrovic da Willian da koci, Marco Silva.
Hukumar kwallon kafar Ingila ta ce United "Ta kasa tsawatarwa 'yan wasanta a lokacin da suke nuna hali na rashin da'a.''
An bai wa kungiyar Old Trafford nan da ranar Litinin 27 ga watan Maris, domin ta kare kanta.
Dan wasan Fulham, Mitrovic na fuskantar dakatarwa mai tsawo, bayan da ake tuhumarsa da ture alkalin wasa, Kavanagh, wanda hakan ya sa ya yi masa jan kati.
United ce ta yi nasara a karawar a Old Trafford, wadda za ta buga zagayen daf da karshe a FA Cup da Brighton a Wembley.
Haka kuma FA ta tuhumi Wolves da nuna halin rashin da'a da mahukuntanta suka nuna daf da za a tashi wasan da ta yi rashin nasara a Leeds United.
An bai wa Matheus Nunes jan kati, koda yake daga baya an soke katin.
FA tana tuhumar 'yan wasa da mahukuntan kungiyar da nuna rashin da' a.











