Wane ne Imran Khan kuma me ake zargin tsohon firaministan na Pakistan da aikatawa?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Ahmen Khawaja and Asad Ali Chaudhry
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- An wallafa
Wane ne Imran Khan?
Ya kasance tsohon ɗan wasan kuriket na duniya, da ya koma ɗan siyasa, kuma ya jagoranci Pakistan wajen samun nasara a Gasar Kofin Duniya a 1992.
Khan da ya fito daga birnin Lahore, ya yi ritaya daga wasan kuriket, inda ya samar da miliyoyin daloli wajen gina asibitin masu cutar kansa domin tunawa da mahaifiyarsa.
Irin gudummawar da yake bayarwa wajen ci gaban al'umma, ta sanya shi shiga harkar siyasa.
Mista Khan ya riƙe muƙamin firaministan Pakistan daga watan Yulin 2018 zuwa Afrilun 2022, da kuma matsayin shugaban jam'iyyar Pakistan Tehreek-e-Insaf PTI.

Asalin hoton, Getty Images
Wane zargin cin hanci ake yi masa?
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasar Pakistan, ta kama Imran Khan a ranar Talata 9 ga watan Mayu, inda take zarginsa da aikata rashawa.
Jami'an gwamnati sun yi zargin cewa Khan da matarsa sun samu fili da kimarsa ta kai miliyoyin daloli a matsayin cin hanci daga wata cibiya da ke harkar gidaje da kuma wata gidauniya.
An yi wa tuhumar laƙabi da Al-Qadir Trust.
Khan da masu taimaka masa sun musanta aikata ba daidai ba.
Tsohon firaministan mai shekara 70, ya ce zarge-zargen na alaƙa da siyasa. Ya kuma zargi jam'iyyun siyasa da haɗa kai da sojojin ƙasar wajen hamɓaras da shi daga mulki.

Asalin hoton, Reuters
Mene ne zargin na Al-Qadir Trust?
Al-Qadir Trust ta kasance gidauniya mai kula da walwala.
Tsohon firaministan da matarsa ta uku, Bushra Wattoo, wadda ake kira da Bushra Bibi, sun kasance shugabannin kwamitin amintattu a gidauniyar.
Imran Khan ya yi alƙawarin gina jami'ar Al-Qadir a Punjab, wani lardi mai ɗumbin jama'a a Pakistan.
Wurin da za a gina jami'ar na da fili mai girman eka 60 a garin Jhelum na Punjab, sai dai abin da aka gina a wurin ba shi da girman gaske.

Asalin hoton, Getty Images
Mene ne haɗin Birtaniya da zargin da ake yi masa?
A ranar 3 ga watan Disamban 2019, Hukumar Hukunta Laifuka ta Birtaniya ta sanar da cewa, an bai wani hamshaƙin mai kuɗi, kuma ɗan kasuwa a Pakistan mai suna Malik Riaz Hussain, kuɗin da ya kai $240m.
Hukumar ta NCA ta ce tana zargi kuɗin na cin hanci ne da aka sanya a asusunsa da ke Birtaniya da aka rufe, inda ta ce za a mayar da kuɗin zuwa Pakistan.
Mista Hussaini ya mayar da martani kan lamarin a shafinsa na Twitter.
"Na sayar da kadarorinmu da muka mallaka a Birtaniya domin biyan Kotun Kolin Pakistan $240m a kan shari'ar da ta shafi garin Bahria," in ji Hussaini a shafinsa na Twitter.
"Sanarwar da NCA ta fitar ta ce batun ba ya nuna cewa aikata hakan laifi ne."
Ta yaya ake zargin an karɓi cin hancin?
Gwamnati mai ci ta yi iƙirarin cewa maimakon a sa $240m a baitul-malin Pakistan, gwamnatin Imran Khan ta yi amfani da kuɗin wajen biyan tarar da kotu ta yi wa mista Hussaini kan zargin mallakar filin gwamnati a farashin ƙasa da na kasuwa a birnin Karachi.
Ministan harkokin cikin gida ya yi zargin cewa mista Hussaini ya bayar da fili a garin Jhelum ga Gidauniyar Al-Qadir domin biyan buƙatarsa.

Asalin hoton, Getty Images
Mene mataki na gaba a Pakistan?
Tun bayan hamɓaras da shi a matsayin firaminista, Imran Khan ya yi ta gudanar da gangami don ganin an gudanar da zaɓe cikin ƙankanin lokaci.
Ana sa ran yin zaɓukan nan gaba a wannan shekara.
Masu taimaka wa Khan sun ce akwai ƙararraki sama da 100 a kansa.
Duk da artabu da masu zanga-zanga ke ci gaba da yi, Imran Khan ya zama sananne a Pakistan, ƙasa mai al'umma miliyan 230.
Mutane da dama sun ce zarge-zargen da ake yi wa tsohon firaministan, kawai za su ci gaba da ƙara masa karɓuwa ne a Pakistan.







