Zaha ya koma buga wasannin aro a Charlotte ta Amurka

Asalin hoton, Getty Images
Wilfried Zaha ya koma buga wasannin aro a gasar tamaula ta Amurka a ƙungiyar Charlotte FC, kan yarjejeniyar zuwa Janairun 2026.
Haka kuma da zarar Zaha ya taka rawar gani, za a iya tsawaita masa zuwa karshen Yunin 2026.
Tsohon ɗan wasan Crystal Palace yana buga wasannin aro a Lyon daga Galatasaray ta Turkiya.
Ya buga wa ƙungiyar Faransa wasa shida a kakar nan, biyar daga ciki a matakin sauyin ɗan wasa.
Zaha, mai shekara 32, ya yi wa Palace karawa 458, shi ne na uku a yawan yi wa ƙungiyar wasanni, wanda ya ci ƙwallo 90.
Ya koma Manchester United a 2013, sai ya sake komawa Selhurst Park kaka ɗaya tsakani a matakin aro.
Ɗan wasan tawagar Ivory Coast ya koma Galatasaray kan yarjejeniyar kaka uku, bayan da yarjejeniyarsa ya kare a Palace a kakar 2023.
A kakarsa ta farko a Turkiya, Zaka ya zura ƙwallo 10 ya bayar da biyar aka zura a raga a wasa 42 lokacin da Galatasaray ta lashe babban kofin tamaula na Turkiya.











