Lookman ya ci ƙwallo biyu a wasan Atalanta da Napoli

Ademola Lookman

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ademola Lookman ne ya zura ƙwallo biyu a raga a wasan Serie A da Atalanta ta doke Napoli 3-0 ranar Lahadi a filin wasa na Diego Armando Maradona.

An yi mamaki da aka ajiye Mateo Retegui a benci, wanda shi ne kan gaba a yawan cin ƙwallaye a Serie A a kakar nan, amma sai Lookman ya taka rawar da ake bukata.

An kuma sa Retegui a karawar ana saura minti 14 a fafatawar da Atalanta ta kai ziyara, wanda ya ci na uku daf da za a tashi, kuma na 11 da ya zura a gasar kenan.

Da wannan sakamakon Atalanta ta koma mataki na biyu a teburin babbar gasar tamaula ta Italiya, amma watakila Inter Milan ta maye gurbinta da zarar ta doke Venezia ranar Lahadi.

Atalanta ta fara cin ƙwallo ta hannun Lookman, bayan samun tamaula daga Charles de Ketelaere daga bugun kwana.

Kaɗan ya rage Napoli ta farke a lokacin da Scott McTominay ya buga ƙwallo, amma sai ta yi faɗi ta yi wajen fili.

Daga nan ne Atalanta ta kara na biyu ta hannun Lookman, sakamakon da ya samu tamaula ta hannun De Ketelaere, wanda ya yanke mutum biyu ya bayar da ƙwallon.

Retegui, wanda ya zura na uku a raga, shi ne ya canji De Ketelaere.