Newcastle na son Mbeumo, Arsenal da PSG na farautar Ndicka

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Newcastle na son dan wasan gaba na Kamaru mai taka leda a Brentford, Bryan Mbeumo, 25, sai dai ta damu kan farashin fam miliyan 60. (Telegraph)

Newcastle din dai ba za ta ci gaba da zawarcin dan wasan tsakiya na Bournemouth Dean Huijsen, 20, bayan gane kurenta kan rashin nasarar da ta yi a shekarar da ta gabata kan dauko dan wasan Ingila Marc Guehi, mai shekara 24 daga Crystal Palace. (i paper)

Manchester United na duba yiwuwar sayo dan wasan baya na Jamus, Jonathan Tah, 29, lokacin bazara, bayan karewar kwantiraginsa da Bayer Leverkusen. (Sky Sports)

Arsenal ka iya fafatawa da Paris St-Germain kan dauko dan mai tsaron gida na Ivory Coast, kuma mai taka leda a Roma, Evan Ndicka mai shekara 24, wanda aka yi wa darajar fam miliyan 34. (Mirror)

Aston Villa na zawarcin dan wasan tsakiya na Belgium Kevin de Bruyne, 33, wanda zai bar Manchester City a karshen kakar wasa. (Football Insider)

Ba lallai Chelsea ta zuba sama da fam miliyan 100, dan dauko dan wasan tsakiya na Argentina, Enzo Fernandez, 24, wanda Real Madrid ta jima ta ke hakilon daukar shi. (Sky Sports)

Manchester United ta amince da yarjejeniyar dauko matashin dan wasan gaba na Faransa Enzo Kana-Biyik, mai shekara 18 daga Le Havre. (Fabrizio Romano)

Bayer Leverkusen na kokarin katange mai kai hari na Jamus Florian Wirtz, kar ya koma Bayern Munich a kakar nan, a bangare guda kuma kungiyoyin Manchester City da Real Madrid na son dan wasan mai shekara 21. (Sky Germany)

A shirye Real Madrid ta ke ta bai wa mai tsaron ragar Ukraine Andriy Lunin, 26, damar barin kulub din a kakar nan, duk da kasancewar dan wasan Chelsea da ta ke son maye gurbin sa da shi, wato Spaniard Kepa Arrizabalaga mai shekara 30 na zaman aro Bournemouth. (Mundo Deportivo)

Aston Villa na zawarcin dan wasan tsakiya na Belgium Kevin de Bruyne, 33, wanda zai bar Manchester City a karshen kakar wasa. (Football Insider)

Crystal Palace za ta so sama da fam miliyan 80, idan har za ta saida dan wasan tsakiya na Ingila Adam Wharton, 21, a kakar nan. (Teamtalk)