An gurfanar da ƙarin mutum 17 kan kisan matar da aka ƙona a Kaduna
Rundunar ‘yansandan Jihar Kaduna ta ce ta kama tare da gurfanar da wasu ƙarin mutane 17 da ake zargi da hannu a kisan gillar matar da aka ƙona a Maraban Jos, inda ta bayyana cewa bincike kan lamarin na ci gaba da gudana.
A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Mansir Hassan, ya fitar, ya ce an gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu a ranar 25 ga Yunin 2026.
Har ila yau, rundunar ta ƙara da cewa bayan kammala binciken farko, an tuhumi wasu mutum 33 da laifin haɗa baki wajen aikata laifin.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa mutum 30 da aka kama a baya sun samu ‘yanci ba tare da wani sharaɗi ba, bayan bincike ya nuna ba su da hannu a kisan.
Rundunar ta ce tana ƙara ƙaimi wajen gano da kama dukkan waɗanda suka shiga ko suka taimaka wajen aikata wannan laifi, tare da jaddada cewa duk wanda aka samu da laifi za a hukunta shi.