Sarauniya Elizabeth II: Shugabannin Afirka suna jimamin rasuwarta

An wallafa

Gimbiyar wancan lokaci Elizabeth ta sauka a otal din Treetops da ke wani yankin karkara na kasar Kenya, mai cike da korayen ganye, da dogayen bishiyoyi da namun dawa, lokacin da mahaifinta, Sarki George VI, ya mutu kuma ta zama Sarauniya tana da shekaru 25.

A shekaru 70 da Sarauniya Elizabeth II ta kwashe tana mulki ta ziyarci kasashen Afirka fiye da 20, kuma a wani lokaci cikin raha a gaban Nelson Mandela, wanda yake murmushi, ta bayyana cewa ta fi "kusan kowa" a Afirka zuwa kasashen nahiyar, abin da ya sa mutanen da ke tare da ita a wancan lokacin suka tuntsire da dariya.

Da yake ta gaji yankuna da dama a nahiyar Afirka yayin da ta zama Sarauniya, a zamaninta ne dukkan kasashe 14 da Birtaniya ta yi wa mulkin suka samu 'yancin kai, inda Ghana ta soma samun nata 'yancin a 1957.

Sarauniya ta kulla dangantaka mai yauki tsakaninta da kasashen na Afirka, galibi ta hanyar kirkirar kungiyar Commonwealth.

A shekarar 1961, an dauki hotonta tana rawa tare da Kwame Nkrumah, wanda ya jagoranci fafutukar neman 'yancin Ghana kuma ya zama shugaban kasar na farko.

Wani muhimmin abu shi ne a bikin nadinta a 1953 ba a yi amfani da kalmar daula ba.

Yanzu, shugabannin kasashen Afirka sun bayyana jimaminsu game da rasuwar Sarauniyar kuma shugaba mafi dadewa ta kungiyar Commonwealth.

Shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta, kasar da tana can ne aka bayyana rasuwar mahaifinta, ya nuna jimaminsa inda ya bayyana ta a matsayin "wata babbar bishiya da ta bauta wa al'umma bil hakki, kuma tana da martaba ba wai kawai a Birtaniya da Commonwealth ba inda Kenya ta kasance mamba har ma duniya baki daya".

Ko da yake dangantaka ta yi tsami tsakanin Zimbabwe da Birtaniya tsawon shekaru, abin da ya sa marigayi shugaban kasar Robert Mugabe ya janye kasarsa daga kungiyar Commonwealth, mutumin da ya gaje shi Emmerson Mnangagwa ya wallafa sakon Tuwita cikin gaggawa kan "ta'aziyyarsa" ga Gidan Sarautar Birtaniya da kuma "al'ummar kasar da kungiyar Commonwealth".

Shugaban Najeriya, kasa mafi girma da Birtaniya ta yi wa mulkin-mallaka a Afirka, Muhammadu Buhari ya rubuta doguwar ta'aziyya a shafinsa na Tuwita, yana mai cewa ya samun labarin mutuwarta "cike da bakin ciki".

"Tarihin Najeriya ba zai taba cika ba ba tare da fadin Sarauniya Elizabeth ll ba, matar da ta yi fice a duniya kuma shugaba ta gari. Ta sadaukar da rayuwarta wajen tabbatar da zaman lafiya a kasarta da kasashen Commonwealth ada ma duniya baki daya."

Kazalika ya yi maraba da hawan Sabon Sarki Charles III kan karagar mulki.

Shi ma shugaban Gabon, Ali Bongo, kasar da Faransa ta yi wa mulkin-mallaka wadda ba ta dade da shiga kungiyar Commonwealth ba, ya bayyana ta'aziyyarsa a sakon da ya wallafa a Tuwita.

Duk da sakonnin ta'aziyyar da shugabannin kasashen nahiyar Afirka, wasu daga cikin kasashen sun bayyana wahalar da suka dade suna sha a karkashin mulkin-mallakar Birtaniya, suna masu cewa an yi mulkin-mallakar ne a madadin gidan sarautar Birtaniya.

Wasu daga cikin sarakuna a nahiyar Afirka su ma sun mika sakon ta'aziyyar su game da rasuwar Sarauniyar Ingila.

Yarima Mangosuthu Buthelezi ya mika sakon ta'aziyyarsa a madadin Sarki Misuzulu KaZwelithini, na masarautar Zulu da ke Afirka ta Kudu.

Ya bayyana "gwaggwabar abotarsa" da Sarki Charles III, inda ya aike da sakon ta'aziyya kai-tsaye a gareshi.

Sarki Misuzulu ya fahimci irin halin da Sarki Charles ya fada a ciki, kasancewar mahaifinsa, Zwelithini, ya rasu a shekarar da ta wuce,  bayan ya shekara 50 a kan mulki.

Sarauniya ta shahara a duniya a matsayin wacce ba ta tsoma baki a harkokin siyasa, sai dai a shekarar 1995 ta yi wani jawabi mai karfi yayin da ta kai ziyara Afirka ta Kudu shekara daya bayan mulkin turawa kalilan masu nuna wariyar launin fata.

Ya yaba wa kasar kan ci gaban da ta samus: "Kun kasance kasar da ta zama abin misali saboda yadda kuka sasanta da juna a duniya, kuma na sake zuwa nan ne domin na ganewa kaina abin mamakin da kuka yi."