Waiwaye: Neman Yahaya Bello ruwa jallo da ƙaruwar hauhawar farashi
Wannan maƙale ce da ke kawo muku muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi.
EFCC na neman tsohon Gwamnan Kogi Yahaya Bello ruwa a jallo

Asalin hoton, @OfficialGYBKogi
Hukumar yaƙi da cin hanci a Najeriya EFCC ta ayyana tsohon Gwamnan Kogi Yahaya Bello a matsayin wanda take nema ruwa a jallo.
Matakin hukumar na zuwa ne 'yan awanni bayan kotu ta ɗage sauraron ƙarar da hukumar ta shigar saboda wanda take zargin bai halarci zaman kotun ba.
Yayin zaman kotun na ranar Alhamis, lauyan EFCC mai suna Kemi Phinro ya faɗa mata cewa "wani mutum da ke da kariya daga tuhuma ne ke bai wa tsohon gwamnan mafaka".
"EFCC na tuhumar Yahaya Bello da zargin halasta kuɗin haram da suka kai naira biliyan 80.2," in ji hukumar cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na zumunta ɗauke da hoton tsohon gwamnan.
Tun ranar Laraba rahotonni suka ce gwamnan Kogi na yanzu Usman Ododo ya fice da Yahaya Bello a motarsa lokacin da jami'an EFCC suka yi wa gidansa tsinke a Abuja.
Gwamnatin Kogi ba ta ce komai ba game da zargin zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.
A watan Janairun shekarar nan ne Yahaya Bello ya miƙa ragamar mulkin jihar ta Kogi da ke tsakiyar Najeriya ga Usman Adodo, bayan ya shekara takwas a ƙarƙashin jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya.
Kotu ta jingine dakatarwar da aka yi wa Ganduje daga APC

Asalin hoton, APC/X
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wata babbar kotun tarayya a Kano ta dakatar da shugabannin jam'iyyar APC a mazaɓar Ganduje a ƙaramar hukumar Dawakin Tofa daga ɗaukan ƙarin mataki a kan dakatar da shugaban jam'iyyar ta ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje.
A wata takardar kotu mai ɗauke da sa hannun magatakardan kotun, Usama Ibrahim Isah, mai shari'ar Abdullahi Muhammad Liman ne ya bayar da umarnin inda ya buƙaci mutanen da ake ƙara da su guji aiwatar da dakatarwar da aka yi wa Ganduje har zuwa lokacin da za a saurari ƙarar da shugaban APC ya shigar a kotu.
Umarnin kotun ya zo ne sa'oi bayan da babbar kotu a Kano ta tabbatar da dakatarwar da aka yi wa Ganduje saboda zarginsa da rashawa.
Kotun ta kuma umarci ɓangarorin da su tsaya kan matsayin da ake kafin taron manyan jam'iyyun APC na mazaɓar ta Ganduje wanda bayansa ne aka dakatar da shugaban jam'iyyar a mazaɓar.
Mai shari'a Liman ya sa ranar 30 ga watan Afrilu a matsayin ranar da za a saurari shari'ar.
Waɗanda ake ƙara sune Haladu Gwanjo da Nalami Mai AC da Muhammadu Baiti da Danmalam Gata da Musa Lado da Laminu Sani Barguna da Umar Sanda da Auwalu Galadima da Abubakar Daudu.
Hauhawar farashi ta kai kashi 33.20 cikin 100 a watan Maris

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar ƙididdiga a Najeriya ta ce hauhawar farashi ta kai kashi 33.20 cikin 100 a watan Maris.
A shafinta na X, hukumar ta ce hauhawar ta ƙaru ne daga kashi 31.7 cikin 100 na watan Fabarairu.
A cewar hukumar, wannan ya nuna hauhawar farashi ta ƙaru da da kashi 11.16 cikin 100 a watan Maris ɗin 2024 idan aka kwatanta da yadda yake a watan Maris na 2023 da ya kasance kashi 22.04 cikin 100.
Kazalika ƙididdigar da NBS ta fitar ta nuna cewa hauhawar farashi a Maris ɗin 2024 ta kai kashi 3.02 cikin 100 saɓanin kashi 3.12 cikin 100 da aka gani a watan Fabarairu.
Hakan na nufin a watan Maris, ƙaruwar farashin kayayyaki ba ta kai wadda aka gani ba a watan Fabarairu.
Za mu iya mayar wa maniyyata rarar kuɗi saboda karyewar dala - NAHCON

Asalin hoton, NAHCON X
Shugaban hukumar Alhazan Najeriya, Alhaji Jalal Ahmad Arabi ya ce akwai yiwuwar hukumar ka iya mayar wa maniyyata rarar kuɗin da suka biya sakamakon karyewar farashin dalar Amurka.
Alhaji Jalal Arabi ya shaida hakan ne a wata hira da kafar sadarwa ta DCL da ke intanet wadda kuma hukumar alhazan Najeriya ta wallafa a shafinta na X, ranar Alhamis.
"Idan misali ranar da muka yi shela dala tana naira 1,000, sai ya zamana kai ranar da ka saka kuɗinka ka saka ne ranar da take naira 900, to ai ka ga akwai rarar naira 100. Wannan naira 100 ya kamata mu mai da maka. Ba mu jira tana ta yin ƙasa ba. To idan kuma ta ƙara yin sama fa?" In ji Jalal Arabi.
Ya ƙara da cewa "indai da rai da lafiya kuma idan dai mu ne a kan kujerar to ba za mu zauna a kan haƙƙin kowa ba da izinin Allah. Za mu tabbatar mun biya wannan rarar."
To sai dai shugaban hukumar ta Alhazan Najeriya bai faɗi lokacin da za a mayar wa da maniyyatan rarar kuɗaɗen nasu ba.
A mafi yawancin lokuta dai hukumar ta Alhazai kan mayar wa alhazai rarar kudaɗen ne bayan kammala aikin Hajji.
A yanzu haka dai naira na ci gaba da samun tagomashi a kan dalar Amurka inda bayanai ke nuna farashin dala a kasuwar bayan fage na tsakanin naira dubu ɗaya da ƙasa da haka.
NLC ta nemi sabon albashi mafi ƙaranci ga ma'aikta na N615,000

Asalin hoton, Getty Images
Kungiyar ƙwadago ta Najeriya NLC ta gabatar da buƙatar ƙarin sabon albashi mafi karanci na N615,000 domin magance kalubalen tattalin arziki da tsadar rayuwa da ma’aikata ke fuskanta a Najeriya.
Shugaban ƙungiyar ne ya tabbatar da hakan ga gidan talabijin na Channels a ranar Lahadi.
An cimma sabon albashi na N615,000 duk wata bayan tattaunawa tsakanin ƙungiyar kwadago ta NLC da TUC ne da nufin rage matsalolin kuɗi da ma’aikatan Najeriya ke fuskanta.
Ƙungiyoyin ƙwadagon sun ce mafi karancin albashi na N30,000 a halin yanzu ba zai iya biyan buƙatun talakawan Najeriya ba, suna masu korafin cewa ba dukkan gwamnoni ne ke biyan albashin ma’aikata na yanzu ba wanda zai ƙare a watan Afrilu, shekaru biyar bayan sohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya rattaba hannu kan dokar mafi karancin albashi ba 2019 inda za a sake duba dokar duk bayan shekaru biyar.
Yadda tsutsa ta janyo wa manoma asarar Naira miliyan 500 a Kano

Asalin hoton, Ismai’l Bagwai
Wasu manoman a karamar hukumar Bagwai na jihar Kano, sun koka kan yadda tsutsa ke lalata musu amfanin gona.
Manoman sun ce sun yi asarar amfanin gona da ta kai kusan Naira miliyan 500.
Sun kuma ce tsutsar ta shafi kusan hekta 1000 na gonakinsu.
Wani manomin tumatir, Bello Idris ya ce suna cikin wahalhalu kan yadda tsutsar ta addabe su.
''Za mu nome tumatir mu sayi taki 50,000, mu kuma sayi maganin feshi 10,000 da man fetur amma duk a banza,'' in ji shi.
Ya yi kira ga gwamnati da ta kawo musu ɗauki da kuma gano inda matsalar take.
Haka-zalika, shi ma Sama'ila Bello mazaunin karamar hukumar Dawakin Tofa, ya ce tsutsar na lalata musu amfanin gona cikin lokaci kankani.
"Muna so gwamnati ta taimaka mana a duba a ɓangaren iri ne ko maganin feshi ne ba a sayar da mai kyau," in ji Bello.

Asalin hoton, Ismai’l Bagwai











