Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Chelsea ta koma zawarcin Osimhen, Manchester United za ta rabu da Christian Eriksen
Napoli ta fara tattaunawa da Manchester United a kan cinikin ɗan wasan tsakiyar Scotland mai shekara 27, Scott McTominay, kuma za ta fi buƙatar ɗaukar sa a matsayin aro. (Times - subscription required)
Manchester United na jiran tayi daga ƙungiyoyin da ke sha'awar ɗaukar ɗan wasan tsakiyar Denmark mai shekara 32, Christian Eriksen, wanda kwangilar sa ke ƙarewa nan da shekara ɗaya. (Sky Sports)
Napoli ta kusa kammala cinikin ɗan wasan tsakiyar Scotland mai shekara 23, Billy Gilmour daga Brighton. (Corriere dello Sport - in Italian)
Chelsea ta sake komawa zawarcin ɗan wasan gaban Napoli mai shekara 25 kuma ɗan Najeriya Victor Osimhen. (Talksport)
Paris St-Germain ta ja da baya daga cinikin ɗan wasan Ingila da Manchester United mai shekara 24, Jadon Sancho kuma tana tunanin janyewa daga neman Osimhen. (i)
West Ham na fatan ɗaukar ɗan wasan Roma kuma ɗan Ingila mai shekara 26, Tammy Abraham kuma ƙungiyar gasar Serie A ɗin ta na shirin rabuwa da ɗan wasan idan aka biya ta £25m. (Gazzetta dello Sport via Football Italia)
Ipswich za ta ɗauki aron ɗan wasan tsakiyar Sweden Jens Cajuste na tsawon shekara ɗaya daga Napoli, bayan Brentford ta janye daga cinikin ɗan wasan mai shekara 25. (Gianluca Di Marzio - in Italian)
Ƙungiyar Al-Qadsiah ta Saudiyya ta gabatarwa ɗan wasan gaban Ingila mai shekara 28, Ivan Toney tayin albashin £15.4m a shekaraa wani yunƙuri na ɗauke shi daga Brentford. (Footmercato - in French)
Real Sociedad ta ƙi amincewa da tayin da Arsenal ta gabatar a kan ɗan wasan tsakiyar Sifaniya mai shekara 28, Mikel Merino, wwanda tuni ya amince da ƙa'idojin kwangila da ƙungiyar ta birnin London. (Times - subscription required)
Ƙungiyar Bologna ta gasar Serie A na zawarcin dan wasan bayan Chelsea, Trevoh Chalobah. Za ta ɗauki ɗan wasan Ingilan mai shekara 25 ne a matsayin aro. (La Gazzetta dello Sport - in Italian)