Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mbappe ya fara da lashe Uefa Super Cup a Real Madrid
Real Madrid ta lashe Uefa Super Cup na 2024/25, bayan da ta doke Atalanta 2-0 ranar Laraba a wasan da suka kara a birnin Warsaw a Poland.
Ƙungiyoyin sun tashi ba ci a minti 45, bayan da suka koma zagaye na biyu ne Real ta fara cin ƙwallo ta hannun Federico Valverde, sannan Kylian Mbappe ya kara na biyu.
Wasan buɗe labulen gasar zakarun kungiyiyin Turai da aka yi kenan tsakanin Real mai Champions League na bara da Atalanta mai Europa League a kakar da ta wuce.
Real Madrid ta ɗauki Kylian Mbappe a bana daga Paris St Germain, don kara karfin ƙungiyar, wanda shi ne na biyu a baya-bayan nan da ya ci ƙwallo a ƙungiyar a wasansa na farko.
Jude Bellingham ya yi wannan bajintar a Real Madrid a wasan La Liga da Athletic Club a Agustan 2023.
Kawo yanzu Mbappe ya ci ƙwallo bakwai a wasan karshe da ya haɗa da ɗaya a Coupe de France a 2021 da ɗaya a UEFA Nations League a 2021 da uku a wasan karshe a gasar kofin duniya a Qatar a 2022 da ɗaya a Trophée des Champions a 2021 Paris St Germain da ɗaya a Uefa Super Cup a 2024.
Real Madrid ta lashe Uefa Super Cup na shida jimilla kenan, wadda ta fafata karo na tara a gasar a tarihi, wadda aka doke ta wasan karshe uku.
Haka kuma Real ta zama ta farko mai Uefa Super Cup shida jimilla, yayin da Barcelona da AC Milan kowacce keda biyar a tarihi.
Kofi na 14 da Ancelotti ya ɗauka kenan jimilla a matakin mai horar da Real Madrid, ya kuma yi kan-kan-kan da irin bajinyar koci, Miguel Munoz a ƙungiyar.
Haka kuma Ancelotti ya ɗauki Uefa Super Cup na huɗu a tarihi, ya haura Pep Guardiola na Manchester City mai uku.
Ƙungiyar da Carlo Ancelotti ke jan ragama ta buga wasan ne, bayan da ta doke Borussia Dortmund 2-0 a Wembley ta lashe Champions League a bara.
Wannan shi ne karon farko da Atalanta ta buga Uefa Super Cup, wadda ta samu damar bayan cin Bayern Leverkusen 3-0 a bara.