Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Chelsea ta bai wa Neto riga mai lamba 19
Sabon ɗan wasan da Chelsea ta ɗauka a bana, Pedro Neto zai yi amfani da riga mai lamba 19 a ƙungiyar.
Ranar Lahadi ɗan wasan na tawagar Portugal ya kammala komawa Stamford Bridge daga Wolverhampton, kan yarjejeniyar da za ta kare a karshen kakar 2031.
Tuni aka gabatar da ɗan wasan a gaban magoya baya a lokacin wasan sada zumunta da Chelsea ta buga da Inter Milan.
Ƴan wasa da yawa sun saka riga mai lamba 19 a Chelsea, wadda aka fi bai wa masu cin ƙwallaye a ƙungiyar.
Digo Costa ya yi amfani da lambar, wanda ya sauya daga 9, bayan da Fernando Torres ya bar Stamford Bridge.
Tore Andre Flo ya saka lamba tara, wanda ya yi kaka uku a Stamford Bridge, bayan da ya koma ƙungiyar a 1997 daga Brann ta Norway.
A lokacin da Jose Mourinho ya horar da Chelsea, Scott Parker da Lassana Diarra sun saka riga mai lamba 19 a ƙungiyar.
Bayan da Diarra ya bar Chelsea zuwa Arsenal, wanda daga baya ya koma Portsmouth da Real Madrid, sai Paulo Ferreira ya ajiye lamba 20 ya karɓi 19.
Demba Ba shima ya saka lamba 19 a Chelsea, wanda daga baya Diego Costa ya karba karkashin Mourinho.
Haka ya ci gaba da amfani da lambar har zamanin koci, Guus Hiddink da kuma Antonio Conte.
Mason Mount ne ya yi amfani da lamba 19 a Chelsea daga 2019/20 zuwa 2022/23, wanda ya koma Manchester United.