Turpin ne raflin wasan Man City da Real Madrid a Champions League

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar ƙwallon kafa ta Turai, UEFA ta sanar da Clement Turpin a matsayin raflin da zai busa wasan Manchester City da Real Madrid ranar Talata.
City, mai rike da kofin Premier League za ta kara da Real Madrid mai Champions League a Etihad a wasan cike gurbin kai wa zagaye na biyu a gasar zakarun Turai.
Real ta kawo wannan matakin sakamakon da ta kare a mataki na 11 a cikin rukuni a Champions League, Ita kuwa City ta 22 ta karkare.
Wannan shi ne karo na takwas da Turpin ɗan kasar Faransa zai busa wasan da ya shafi Real Madrid a Champions League.
Real Madrid tana matakin farko a kan teburin La Liga, wadda ta tashi 1-1 ranar Asabar da Atletico Madrid a wasan hamayya na ƴan birnin Sifaniya.
Cty kuwa tana ta biyar a teburin Premier League, wadda ta kai zagaye na biyar a FA Cup, sakamakon doke Leyton Orient 2-1 a FA Cup ranar Asabar.
Wasannin da Turpin ya yi rafli a karawa da Real a Champions League:
- Real Madrid 4-0 Ludogorets (Wasan cikin rukuni 2014/15)
- Roma 0-2 Real Madrid (Wasan cikin rukuni 2018/19)
- Real Madrid 3-2 Inter (Wasan cikin rukuni 2020/21)
- Chelsea 1-3 Real Madrid (Kwata fainalzagayen farko 2021/22)
- Liverpool 0-1 Real Madrid (Wasan karshe 2021/22)
- Napoli 2-3 Real Madrid (Wasan cikin rukuni 2023/24)
- Bayern Munich 2-2 Real Madrid (Daf da karshe wasan farko (2023/24)






