Ban damu da fuskantar kalubale ba kan horar da Real - Ancelotti

Asalin hoton, Getty Images
Carlo Ancelotti ya ce yana maraba da duk wani matsi, saboda horar da Real Madrid, kuma bai damu ba kan raɗe-raɗin makomarsa a ƙungiyar.
Ancelotti ya lashe La Liga biyu da Champions League biyu a kaka uku tun bayan da ya koma Real Madrid daga Everton a 2021, amma yana fuskantar kalubale a kakar nan.
Real Madrid ta yi ban kwana da Champions League a zagayen kwata fainal, bayan da Arsenal ta doke ta 5-1 gida da waje a kakar nan, duk da ita ce mai rike da kofin.
Haka kuma Real Madrid mai rike da La Liga na bara tana mataki na biyu a teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya da tazarar maki huɗu tsakani da Barcelona ta ɗaya, kuma saura wasa shida-shida a kammala kakar nan.
Rashin nasarar da Real ta yi a hannun Arsenal ya sa ake danganta Ancelotti da zai karɓi aikin horar da tawagar Brazil, shi kuwa Xabi Alonso zai bar Bayern Leverkusen, domin maye gurbin ɗan Italiya a Santiago Bernabeu.
An tambayi Ancelotti ko yana fuskantar matsi, sai ya ce: ''Ƙungiyar ta kwan da sanin cewar muna mawuyacin hali a kakar nan, fiye da yadda muka taka rawar gani a bara.
Real Madrid za ta fafata da Barcelona ranar Asabar a wasan karshe a Copa del Rey, sannan za su sake karawa a La Liga cikin watan Mayu.
An tambayi kocin ko idan ya lashe La Liga da Copa del Rey a bana, zai samu saukin matsi a Real Madrid, sai Ancelotti ya ce: ''A ƙwallon kafa komai zai iya faruwa, bana mamakin wani abun, komai zai iya faruwa.''











