Neymar ba zai yi wasan Bayern ba a Champions League

Neymar

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Neymar ba zai yi wa Paris St-Germain wasan Champions League da za ta ziyarci Bayern Munich in ji koci, Christophe Galtier.

Dan kwallo Brazil ya ji raunin da sai daukar shi aka yi a gadon daukar marasa lafiya a fafatawar da PSG ta doke Lille 4-3 ranar 19 ga watan Fabrairu.

''Ba zai yi mana wasa biyu nan gaba da za mu buga ba,'' in ji Galtier.

''Saboda haka mai makon mu yi wasa da 'yan kwallo biyu da ke buga tsakiya, za mu saka uku, sai masu cin kwallo su koma biyu.''

Kenan Kylian Mbappe da Lionel Messi, sune daga can gaba a wasa na biyu a Champions League da za su fafata ranar Laraba a Jamus.

Sun kara ranar 14 ga watan Fabrairu a Faransa, inda Bayern ta ci 1-0, kuma Kingsley Coman ne ya zura kwallon a raga.

Haka kuma PSG na fama da wasu 'yan wasan da ke jinya tun kafin wasanta da Nantes a Ligue da suka hada da Renato Sanches da kuma Presnel Kimpembe.