Afcon 2023: An dakatar da ƙyaftin ɗin Mali buga wasa huɗu

An wallafa

An dakatar da ƙyaftin ɗin Mali, Hamari Traore daga buga wasa hudu, bayan da aka same shi da laifin rashin ɗa'a ga alƙalin wasa.

An bai wa ɗan wasan mai shekara 32 jan kati, bayan tashi karawar da Ivory Coast ta doke su a kwata fainals a Afcon 2023 ranar 3 ga watan Fabrairu.

Sai ƴan wasa ne suka janye Traore lokacin da yake ƙalubalantar alƙalin wasa, Mohamed Adel daga Masar a karawar da suka yi rashin nasara 2-1, bayan ƙarin lokaci, yayin da aka ta ture-ture tsakanin ƴan wasa da alƙalai.

An jinkirta rabin hukuncin da zai ji zuwa shekara ɗaya.

Cikin hukuncin da Caf ta yanke, an ci tarar hukumar ƙwallon ƙafar Mali $10,000 kan halin rashin ɗa'a da ƴan wasanta suka nunawa alƙalan tamaula.

Haka kuma an ci tarar hukumar ƙwallon kafar Ivory Coast $5,000 itama kan rashin kirki da ƴan wasanta suka nuna a fafatawar.

Caf ta kuma dakatar da cin tarar ɗan wasan Senegal, Krepin Diatta, bayan da aka same shi da laifin yin kalaman da ba su da ce ba, bayan da Ivory Coast ta fitar da Senegal a zagayen ƴan 16.

An dakatar da ɗan ƙwallon mai shekara 24 wasa huɗu da cin tarar $10,000.

An kuma ci tarar hukumar ƙwallon ƙafa ta Senegal $5,000 kan halin rashin ɗa'a da ƴan wasanta suka nuna.