Arsenal da Newcastle na son Evanilson, Real Madrid na nazari kan James

An wallafa

Arsenal da Newcastle sun tura masu nemo musu 'yanwasa, domin duba wasan mai kai hari, na Porto, Evanilson, dan Brazil mai shekara 24, a karshen mako, kuma dukkanin wakilan kungiyoyin biyu sun duba abokin wasansa a kungiyar Alan Varela danwasan tsakiya na Argentina mai shekara 22. (HITC)

Newcastle za ta koma zawarcin mai tsaron ragar Arsenal da Ingila Aaron Ramsdale, a bazaran nan saboda tana son samun matashin gola. (Mail)

Haka kuma Newcastle din na shirin samun tayi daga Arsenal da Tottenham, wanda ya kai fam miliyan 100, a kan mai kai hari Alexander Isak dan Sweden, yayin da kungiyoyi ke neman ribatar bukatar halin da Newcastle din take ciki na neman kudaden da za ta sayi sababbin 'yan wasa ba tare da ta saba ka'idar kashe kudade ba. (Sun)

An fada wa Tottenham da Newcastle cewa dole duk wadda ke son tsohon danwasan tsakiya na tawagar Ingila ta 'yan kasa da shekara 21 Morgan Gibbs-White, mai shekara 24, daga Nottingham Forest, ta biya sama da fam miliyan 50, wanda za ta sayar dole saboda rashin kudi. (Football Insider)

Dole ne West Ham ta biya akalla fam miliyan 60 idan tana son danwasan tsakiya na Everton da Belgium Amadou Onana mai shekara 22. (Football Insider)

Ana sa ran Manchester City ta sayar da danwasanta na tsakiya Kalvin Phillips, na Ingila a bazara a kan kusan fam miliyan 30. (Mail)

Liverpool, daTottenham da kuma AC Milan za su yi gogayya wajen zawarcin dan bayan Fulham Tosin Adarabioyo, dan Ingila, wanda kwantiraginsa zai kare a bazaran nan. (Sun)

Real Madrid na nazarin sayen dan bayan Chelsea da Ingila Reece James, to amma bisa ga dukkan alamu cinikin zai yi tsauri saboda yana da sauran shekara hudu a kwantiraginsa.(Fichajes )

Watakila Marcos Alonso ya bar Barcelona, a bazaran nan ba tare da wani kwantiragi a kansa ba, yayin da shi ma Sergi Roberto zai iya tafiya a kyauta. (Fabrizio Romano)

Neymar, na shirin komawa kungiyar Santos ta kasarsa Brazil a 2025 lokacin da kwantiraginsa da Al-Hilal ta Saudiyya zai kare. (Goal)

Barcelona ta hakura da neman matashin danwasan Palmeiras da Brazil Estevao Willian, mai shekara 16, wanda ake yi wa lakabi da 'Messinho', inda yanzu Chelsea da Paris St-Germain suka rage a matsayin manyan masu zawarcinsa. (Sport)